عَنْ أَنَسٍ رضي الله عنه:
أَنَّ نَفَرًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سَأَلُوا أَزْوَاجَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ عَمَلِهِ فِي السِّرِّ؟ فَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا أَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، وَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا آكُلُ اللَّحْمَ، وَقَالَ بَعْضُهُمْ: لَا أَنَامُ عَلَى فِرَاشٍ، فَحَمِدَ اللهَ وَأَثْنَى عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا بَالُ أَقْوَامٍ قَالُوا كَذَا وَكَذَا؟ لَكِنِّي أُصَلِّي وَأَنَامُ، وَأَصُومُ وَأُفْطِرُ، وَأَتَزَوَّجُ النِّسَاءَ، فَمَنْ رَغِبَ عَنْ سُنَّتِي فَلَيْسَ مِنِّي».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1401]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun tambayi matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikinsa a ɓoye? sai sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba, sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba, sashinsu ya ce: Ba zan yi bacci akan shinfiɗa ba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi, sai ya ce: "Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1401]
Wasu mutane cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun zo ɗakunan matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, suna tambaya game da ibadarsa a ɓoye a cikin gidansa, lokacin da aka ba su labari kamar cewa su sunga ƙanƙantarta, sai suka ce: Wane mu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi- ? haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa da abinda ya jinkirta, saɓanin wanda bai san faruwar gafara gare shi ba to yana buƙatuwa zuwa kai matuƙa a cikin ibada wataƙila ya sameta. Sannan sashinsu ya ce: Ba zan auri mata ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan ci nama ba. Sashinsu kuma ya ce: Ba zan yi bacci a kan shinfiɗa ba. Sai hakan ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi fushi, ya yi wa mutane huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi yabo gare shi ya ce: Menene sha'anin wasu mutane ne sun ce kaza da kaza?! Na rantse da Allah lallai cewa nine mafi tsoronku ga Allah kuma mafi taƙawarku gare shi, sai dai cewa ni ina bacci dan in samu ƙarfi akan tsayuwar (dare), kuma ina buɗe baki dan in samu ƙarfin azimi, kuma ina auren mata, wanda ya bijire daga hanyata kuma ya ga cika a waninta, ya riƙi hanyar wanina to ba ya tare da ni.