+ -

عن عبد الله بن عباس رضي الله عنهما قال: قدم رسول الله صلى الله عليه وسلم المدينة، وهم يُسلفون في الثمار: السنة والسنتين والثلاث، فقال: «من أسلَفَ في شيء فليُسلف في كيل معلوم، ووزن معلوم، إلى أجل معلوم».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Abbas Allah ya yarda da shi zuwa ga Annabi: ya iso Madina suna bada rancen kayan gona Shekara daya shekara biyu, har uku ma, sai ya ce: "Duk wanda zai yi rancen wani abu to yai rance cikin Sanannen Ma'auni, da kuma Mizani Sananne, kuma zuwa lokaci Sananne"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi ya iso Madina ysns mai hijira, sai ya sami mutanen Madina Ma'abota uka ne da kayan gona, kuma suna bada rancen sa kuma suna jinkirta kudinsa a wasu kayan gona har tsawon shekara, ko shekara biyu ma, ko shekara uku, sai ya tabbatar musu da wannan Mua'malar tasu kuma bai sanya a Matsayin cinikin abinda mai siyarwa bashi da shi ba wanda hakan yakan kai zuwa cinkin kasada, domin bashi yana kan wanda ya ci kuma wajibi ne, sai dai Annabi yai musu bayanin hukunce hukuncen Muamala da zai raba su da rigima da kuma husuma wanda watakila hakan yakaisu tsawon lokaci a bashin, sai ya ce: Duk wanda ya ranci wani abu to ya kiyaye shi da gwargwadonsa da Ma'auni da sikeli, na sharia wadanda suke sanannu, kuma ya hada shi da lokaci sananne, har a iya sanin gwargwadonsa da kuma lokacinsa, daga nan husuma da rigima da kuma Jayayya, kuma Mai saye an bashi hakkinsa cikin Aminci.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin