عَن عبدِ اللهِ بن خُبَيب رضي الله عنه أنه قال:
خَرَجْنَا فِي لَيْلَةٍ مَطِيرَةٍ وَظُلْمَةٍ شَدِيدَةٍ، نَطْلُبُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ؛ يُصَلِّي لَنَا، قَالَ: فَأَدْرَكْتُهُ، فَقَالَ: «قُلْ»، فَلَمْ أَقُلْ شَيْئًا، ثُمَّ قَالَ: «قُلْ»، فَلَمْ أَقُلْ شَيْئًا، قَالَ: «قُلْ»، فَقُلْتُ: مَا أَقُولُ؟ قَالَ: «{قُلْ هُوَ اللهُ أَحَدٌ} وَالْمُعَوِّذَتَيْنِ حِينَ تُمْسِي وَتُصْبِحُ ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، تَكْفِيكَ مِنْ كُلِّ شَيْءٍ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي] - [سنن الترمذي: 3575]
المزيــد ...
Daga Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce:
Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3575]
Sahabi mai girma Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin: Cewa sun fita a dare mai yawan ruwa, kuma duhu ya kasance mai tsanani dan neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; Domin ya yi musu sallah, sai suka same shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka ce" wato ka karanta, bai karanta komai ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake fada masa, sai Abdullahi ya ce: Mezan karanta ya Manzon Allah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka karanta Surat Al-Ikhlas {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai}, da Falaki da Nasi {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina nemn tsari da Ubangijin mutane}, a lokacin yammaci, da lokacin safiya, sau uku za su kiyayeka daga kowanne sharri, kuma zasu kareka daga kowanne mummunan abu.