+ -

عَنْ عَلِيٍّ رضي الله عنه:
أَنَّ فَاطِمَةَ رَضيَ اللهُ عنْها أَتَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ تَشْكُو إِلَيْهِ مَا تَلْقَى فِي يَدِهَا مِنَ الرَّحَى، وَبَلَغَهَا أَنَّهُ جَاءَهُ رَقِيقٌ، فَلَمْ تُصَادِفْهُ، فَذَكَرَتْ ذَلِكَ لِعَائِشَةَ، فَلَمَّا جَاءَ أَخْبَرَتْهُ عَائِشَةُ، قَالَ: فَجَاءَنَا وَقَدْ أَخَذْنَا مَضَاجِعَنَا، فَذَهَبْنَا نَقُومُ، فَقَالَ: «عَلَى مَكَانِكُمَا» فَجَاءَ فَقَعَدَ بَيْنِي وَبَيْنَهَا، حَتَّى وَجَدْتُ بَرْدَ قَدَمَيْهِ عَلَى بَطْنِي، فَقَالَ: «أَلاَ أَدُلُّكُمَا عَلَى خَيْرٍ مِمَّا سَأَلْتُمَا؟ إِذَا أَخَذْتُمَا مَضَاجِعَكُمَا -أَوْ أَوَيْتُمَا إِلَى فِرَاشِكُمَا- فَسَبِّحَا ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ، وَاحْمَدَا ثَلاَثًا وَثَلاَثِينَ، وَكَبِّرَا أَرْبَعًا وَثَلاَثِينَ، فَهُوَ خَيْرٌ لَكُمَا مِنْ خَادِمٍ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 5361]
المزيــد ...

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Faɗima - Allah Ya yarda da ita - ta zo wajen Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - tana kawo ƙarar abinda take gamuwa da shi a hannunta na daka, kuma labari ya isar mata cewa wani bawa ya zo masa, bata same shi ba, sai ta ambaci hakan ga A'isha, lokacin da ya dawo sai A'isha ta ba shi labari, (Aliyu) ya ce: Sai ya zo mana alhali mun kwanta, sai muka tafi muka tashi, sai ya ce: "Ku zauna a wurinku" sai ya zo sai ya zauna tsakani na da ita, sai naji sanyin diga-digansa akan cikina, sai ya ce: "Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5361]

Bayani

Faɗima - Allah Ya yarda da ita - 'yar manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - takai koken abinda take fama dashi na gurbin kayan niƙan da take niƙawa, lokacin da ribatattu suka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ta tafi zuwa gare shi zata tambaye shi ɗan aiki daga waɗannan ribatattun; dan ya tsaya a matsayinta akan ayyukan gida, sai dai cewa bata sameshi a gidansa ba, sai ta samu A'isha - Allah Ya yarda da ita -, sai ta bata labarin hakan, Lokacin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi dawo sai Nana A'isha ta ba shi labarin zuwan Faɗima wurin shi dan ta tambaye shi ɗan aiki ne, sai Annbi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo wurin Nana Faɗima da Aliyu - Allah Ya yarda da su - a gidansu alhali su suna kan shinfiɗa suna shirin barci, sai ya zauna tskaninsu har Aliyu - Allah Ya yarda da shi - ya ji sanyin diga-digan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan cikinsa, sai ya ce: Shin bana sanar daku mafi alheri daga abinda kuka tanbayeni ba akan na baku ɗan aiki? Suka ce: Eh, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kun kwanta dan yin bacci da daddare, to ku yi kabbara sau talatin da huɗu, da faɗin: Allahu Akbar, ku yi tasbihi sau talatin da uku, da faɗin: Subhanallahi, ku yi hamdala sau talatin da uku, da faɗin: Alhamdulillah; to wannan zikirin shi ne mafi alheri gareku daga ɗan aiki.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الصربية الرومانية Malagasy الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so dawwama akan wannan zikirin mai albarka, an ruwaito cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - bai bar wanna wasiyyar ta Annabi ba, mai ƙunsar (abubuwan alheri) har daren da aka yi Siffin.
  2. Wannan zikirin ba'a faɗarsa sai a baccin dare kawai, kuma lafazinsa a wurin Muslim daga riwayar Mu'azu daga Shu'uba "Idan kuka kwanta da daddare".
  3. Idan musulmi ya manta wannan zikirin a farkon dare sannan ya tina shi a ƙarshensa to babu laifi; domin cewa Aliyu - Allah Ya yarda da shi - maruwaicin hadisin yana cewa shi ya manta faɗarsa a daren Siffin a farkon daren sai ya tina sai ya faɗeshi kafin Asuba.
  4. Mihlab ya ce; A cikinsa akwai cewa mutum ya ɗora iyalansa kan abinda ya ɗora kansa aikai na fifita lahira akan duniya idan sun kasance suna da iko akan hakan.
  5. Ibnu Hajar al’Asƙalani ya ce: Wanda ya lazimce shi ba zai cutu da yawan aiki ba kuma ba zai wahalar da shi ba koda gajiya ta faru gare shi.
  6. Al’Aini ya ce: Ta fuskar alherin kodai ana nufin shi yana rataye da lahira ne shi kuma ɗan aiki da duniya, lahira kuwa ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa, ko kuma ana nufin dangane da abinda ta nema da cewa ikon da zata samu ya zama shi ne mafi karfi akan aikin da dan aiki zai yi mata.