kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Duk wanda ya sauka wani masauki, sai ya ce: Ina neman tsarin kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin da ya halitta, to, babu abin da zai cutar da shi har ya bar wannan masaukin
عربي Turanci urdu
'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi
عربي Turanci urdu
Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba
عربي Turanci urdu
Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa
عربي Turanci urdu
"Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya ciyar da mu kuma ya Shayar da mu, kuma ya isar mana kuma ya bamu Makwanci, Saboda da yawa wanda babu mai isar masa ko mai bashi makwanci"
عربي Turanci urdu
Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki
عربي Turanci urdu
Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku
عربي Turanci urdu
Wani mutum ya zo wurin Annabi –sallal Lahu alaihi wa sallama- ya ce: Ya Manzon Allah, Ina son tafiya, don haka ka azurta ni, sai ya ce: “Allah Ya azurta ku da takawa. : Ka warkar da ni, ya ce: "Kuma ka kyautata maka a duk inda kake
عربي Turanci urdu
Manzon Allah ya kasance idan yayi tafiya yana neman tsarin Allah daga Wahalar Tafiya, da Mummunar Dawowa, da tabarbarewar Yanayi, da kuma Addu'ar wanda aka Zalunta, da kuma Mummunan gani a cikin Ahali da Dukiya"
عربي Turanci urdu
"Ya Kasance idan ya ga jinjirin wata yakan ce: Ya Ubangiji ka saukar mana shi a gare mu da aminci da kuma Imani"
عربي Turanci urdu
Abu Saleh Ya kasance yana Umartarmu idan dayan mu zai bacci ya kwanta akan bangaren sa na dama
عربي Turanci urdu
Lallai Waxan nan Ayoyi Allah ya turo su, ba wai sun kasance saboda Mutuwa wani Mutum bane ko rayuwarsa, sai dai Allah yana aiko su don ya tsorata bayinsa, to idan kuka ga wani abu daga cikin su to zabura zuwa Anbaton Allah da roqonsa da kuma neman gafararsa"
عربي Turanci urdu
Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi
عربي Turanci urdu
An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba
عربي Turanci urdu