عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«رَغِمَ أَنْفُ رَجُلٍ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ، وَرَغِمَ أَنْفُ رَجُلٍ دَخَلَ عَلَيْهِ رَمَضَانُ ثُمَّ انْسَلَخَ قَبْلَ أَنْ يُغْفَرَ لَهُ، وَرَغِمَ أَنْفُ رَجُلٍ أَدْرَكَ عِنْدَهُ أَبَوَاهُ الكِبَرَ فَلَمْ يُدْخِلاَهُ الجَنَّةَ».
[صحيح] - [رواه الترمذي وأحمد] - [سنن الترمذي: 3545]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 3545]
Mummunar addu'ar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan nau'i uku da turbuɗe hancinansu da turɓaya daga ƙasƙanci da wulaƙanci da kuma taɓewa. Nau'i na farko: Wanda aka ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wurinsa bai yi masa salati ba da faɗinsa: tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ko makamancinsa. Na biyu: Wanda ya riski watan Ramadan sannan watan ya ƙare ba’a gafarta masa ba saboda gazawarsa a aikata aikin ɗa'a. Na uku: Mutumin da tsufa ya riski iyayensa a wurinsa amma ba su zama sababi a cikin shigarsa aljanna ba dan saɓawarsa da kuma gazawarsa a kan haƙƙinsu.