عَنْ عَبْدَ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ العَاصِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا، قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّكَ لَتَصُومُ الدَّهْرَ، وَتَقُومُ اللَّيْلَ؟»، فَقُلْتُ: نَعَمْ، قَالَ: «إِنَّكَ إِذَا فَعَلْتَ ذَلِكَ هَجَمَتْ لَهُ العَيْنُ، وَنَفِهَتْ لَهُ النَّفْسُ، لاَ صَامَ مَنْ صَامَ الدَّهْرَ، صَوْمُ ثَلاَثَةِ أَيَّامٍ صَوْمُ الدَّهْرِ كُلِّهِ»، قُلْتُ: فَإِنِّي أُطِيقُ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ، قَالَ: «فَصُمْ صَوْمَ دَاوُدَ عَلَيْهِ السَّلاَمُ، كَانَ يَصُومُ يَوْمًا وَيُفْطِرُ يَوْمًا، وَلاَ يَفِرُّ إِذَا لاَقَى».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1979]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan al-Aas - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai kai kana azimi tsawon shekara, kuma kana tsayuwar dare?", sai na ce: Eh, ya ce: "Lallai kai idan ka aikata hakan ido zai yi rauni saboda shi, kuma zuciya zata gajiya saboda hakan, Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa", sai na ce: Lallai cewa ni zan iya sama da hakan, ya ce: "To ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi -, ya kasance yana azimtar yini kuma ya sha yini, kuma ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1979]
(Labari) ya kai ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Abdullahi ɗan Amr - Allah Ya yarda da shi - ya kasance yana jeranta azimi ba ya ajiyewa tsawon shekara, kuma yana sallar dare gaba ɗayansa ba ya bacci, sai ya hana shi daga hakan, kuma ya ce masa: Ka yi azimi kuma ka huta, ka yi sallar dare kuma ka yi bacci. Kuma ya hane shi daga jeranta azimi da tsayuwar dare gaba ɗayansa, kuma ya ce masa: Lallai cewa kai idan ka aikata hakan idanka zai yi rauni saboda shi zai yi kogo zai shige, kuma zuciyarka zata gaji ta ƙosa saboda haka; babu azimi (ga) wanda ya azimci shekara; inda cewa shi bai samu ladan azimin ba dan saɓawa hani, kuma bai buɗe baki ba domin cewa shi ya kame. Sannan ya shiryar da shi zuwa azimin kwana uku a kowane wata shi ne azimin shekara; domin kowace rana (kwatankwacin ladan) kwanaki goma ne, kuma hakan shi ne mafi ƙarancin riɓanyawa ga kyakkyawa. Sai Abdullahi ya ce: Lallai ni zan iya sama da hakan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: To sai ka yi azimin (Annabi) Dawud - aminci ya tabbata agare shi - shi ne mafificin azimi, ya kasance yana azimin yini kuma yana hutawa yini, kuma ya kasance ba ya gudu idan ya gamu da maƙiya; domin tsarin aziminsa ba ya raunana jikinsa ba.