عَنْ أَبِي سَعِيدٍ الْخُدْرِيِّ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«مَنْ صَامَ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللهِ بَاعَدَ اللهُ وَجْهَهُ عَنِ النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1153]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id Alkhudr - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa:
"Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1153]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya azumci wani yini a yaƙi, an ce a yaƙi da waninsa yana mai ikhlasi ga Allah dan neman sakamako da lada daga Allah; to lallai Allah da falalarsa Zai nisantar da tsakaninsa da tsakanin wuta (tsawon) shekara saba'in.