عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم : «إن أَحَبَّ الصيام إلى الله صِيَامُ داود، وأحب الصلاة إلى الله صلاة داود، كان يَنَامُ نِصْفَ اللَّيْلِ، وَيَقُومُ ثُلُثَهُ، وَيَنَامُ سُدُسَهُ، وكان يصوم يومًا ويُفطِرُ يومًا».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Amr Dan Asi - Allah ya yarda da su - " Lallai cewa Mafi Soyuwar Azumi A wajen Allah shi ne Azumin Annabi Dauda, kuma Mafi soyiwar Sallah Ita ce Sallar Annabi Dauda, ya kasance yana bacci rabin Dare, kuma ya tashi Daya bisa ukun Dare, kuma ya kara Bacci a Daya bisa Shidan Dare, kuma ya kasance yana Azumi yau kuma gobe ya Huta"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Abdullahi Dan Amr -Allah ya yarda da shi- yana bamu Labari a cikin wannan Hadisin cewa Mafi soyuwar Azumi da kuma Sallah izuwa ga Allah shi ne Azumin Annabi Dauda Aminci Allah a gare shi kuma cewa shi yanayin Azumi yau gobe kuma yayi buda baki; sabidasamun damar yin Ibada da kuma bawa jikinsa Hutu, kuma ya kasance yanayin Bacci a rabin Dare kuma ya tashi cikin Nishadi yana mara nauyin jiki zuwa Ibada, sai ya yi Sallah Daya bisa Ukun Dare Sannan ya yi bacci daya bisa shidan Dare na Karshe; don ya kasance yayi Nishadi don yin Ibada farkon Dare, kuma wannan shi ne Salo shi ne wanda Annabi ya Kwadaitar da mu.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin