عَنْ عَائِشَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«تَحَرَّوْا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي الوِتْرِ مِنَ العَشْرِ الأَوَاخِرِ مِنْ رَمَضَانَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2017]
المزيــد ...
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2017]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yin ƙoƙari a nema da kirdadon daren lailatul-ƙadr da yawaita aiki na gari, shi ne mafi ƙauna ya kasance a darare na mara daga goman ƙarshe a Ramadan a kowace shekara, sune: Ashirin da ɗaya, da ashirin da uku, da ashirin da biyar, da ashirin da bakwai, da ashirin da tara.