عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَجْتَهِدُ فِي الْعَشْرِ الْأَوَاخِرِ مَا لَا يَجْتَهِدُ فِي غَيْرِهِ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1175]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita -:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1175]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ya zo na Ramadan yana ƙoƙari a cikinsu da yin ibada da ɗa'a, kuma yana kai matuƙa a cikin nau'ikan alherai da sinfofin ayyukan kirki da ibadu mafi yawa daga abinda yake ƙoƙari a cikin waninsa; hakan dan girma da falalar waɗancan dararen da kuma dan neman daren Lailatul Ƙadr.