عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا:
أَنَّ رِجَالًا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أُرُوا لَيْلَةَ القَدْرِ فِي المَنَامِ فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَرَى رُؤْيَاكُمْ قَدْ تَوَاطَأَتْ فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ، فَمَنْ كَانَ مُتَحَرِّيهَا فَلْيَتَحَرَّهَا فِي السَّبْعِ الأَوَاخِرِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2015]
المزيــد ...
Daga Ɗan Umar Allah Ya yarda da su:
Cewa wasu mazaje daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - an nuna musu daren Lailatul-ƙadr a cikin mafarki a bakwan ƙarshe, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2015]
Wasu mazaje daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun gani a cikin mafarki cewa daren Lailatul-ƙadr yana kasancewa ne a ƙarshen daren bakwai na Ramadan. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ina ganin mafarke-mafarkenku haƙiƙa sun dace a bakwan ƙarshe na Ramadan, wanda ya kasance yana nufinsa, yana mai kwaɗayi akan nemansa, to sai ya yi ƙoƙari a kardadonsa da nemansa da yawaitawa daga aiki na gari shi ya fi ƙaunar ya zama a bakwan ƙarshe, shi yana farawa ne daga daren ashirin da huɗu idan watan Ramadan ya zama kwana talatin ne, kuma daren ashirin da uku yana farawa ne idan watan ya zama mai kwana ashirin da tara ne.