عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْهَا قَالَتْ:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ الْعَشْرُ أَحْيَا اللَّيْلَ، وَأَيْقَظَ أَهْلَهُ، وَجَدَّ وَشَدَّ الْمِئْزَرَ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1174]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1174]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe na Ramadan ya shiga zai rayar da dukkan dare da nau'ikan ayyukan ɗa'a, kuma ya farkar da iyalansa dan yin sallah, ya yi ƙoƙari a cikin ibada ƙari akan al'adarsa, ya duƙufa gareta, kuma ya nisanci matansa.