عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ:
أَوْصَانِي خَلِيلِي صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِثَلاَثٍ: صِيَامِ ثَلاَثَةِ أَيَّامٍ مِنْ كُلِّ شَهْرٍ، وَرَكْعَتَيِ الضُّحَى، وَأَنْ أُوتِرَ قَبْلَ أَنْ أَنَامَ.  
                        
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1981]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci. 
                                                     
                                                                                                    
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1981]                                            
                        Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa masoyinsa kuma abokinsa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi  masa wasicci kuma ya alkawaranta masa ɗabi'u uku:
Na farko: Azimin kwana uku a kowane wata.
Na biyu: Raka'a biyu ta walaha a kowace rana.
Na uku: Witiri kafin bacci; hakan ga wanda ya ji  tsoron kada ya farka a ƙarshen dare.