عَنْ سَهْلِ بْنِ سَعْدٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«لَا يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1098]
المزيــد ...
Daga Sahl ɗan Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1098]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mutane ba za su gushe ba a cikin alheri muddin dai sun gaggauta buɗa baki a azimi, bayan tabbatar da faɗuwar rana; hakan dan ruko da sunna, da tsayuwa a iyakarta.