عَنِ الحُسَينِ بنِ عَلِيٍّ بنِ أَبِي طَالِبٍ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«الْبَخِيلُ مَنْ ذُكِرْتُ عِنْدَهُ فَلَمْ يُصَلِّ عَلَيَّ».
[صحيح] - [رواه الترمذي والنسائي في الكبرى وأحمد] - [السنن الكبرى للنسائي: 8046]
المزيــد ...
Daga Husaini ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib - Allah Ya yarda da su (Husain da Ali) - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba".
[Ingantacce ne] - - [السنن الكبرى للنسائي - 8046]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsoratar akan barin salati gare shi a halin jin sunansa ko alkunyarsa ko siffarsa, ya ce: Marowaci mai cikakkiyar rowa (shi ne) wanda aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba; hakan saboda wasu al'amura:
Na farko: Cewa hakan rowa ce, da wani abun da ba ya asara saboda shi kaɗan ne ko mai yawa, kuma ba ya bada wata dukiya, kuma ba ya yin wani ƙoƙari.
Na biyu: Cewa shi ya yi wa kansa rowa kuma ya haramta mata ladan salati ga Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa shi haƙiƙa ya yi rowa saboda hanuwarsa daga salati gare shi, kuma ya hanu daga bada haƙƙin da bada shi ya wajaba akansa dan ruko da umarni kuma ake samun lada da shi.
Na uku: Cewa salati gare shi a cikinsa akwai bada haƙƙin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, shi ne wanda ya sanar damu, kuma shi ne wanda ya shiryar damu, shi ne wanda ya kiramu zuwa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - kuma ya zo mana da wannan wahayin, da kuma wannan shari'ar, shi ne sababin shiriyarmu - bayan Allah - alhrerinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - wanda bai yi masa salati ba zai zama haƙiƙa ya yi wa kansa rowa, kuma ya yi rowa ga AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da wani haƙƙin da yana daga mafi ƙasan haƙƙoƙinsa.