عن عُثْمَانَ بْنَ أَبِي الْعَاصِ رضي الله عنه:
أنه أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللهِ، إِنَّ الشَّيْطَانَ قَدْ حَالَ بَيْنِي وَبَيْنَ صَلَاتِي وَقِرَاءَتِي يَلْبِسُهَا عَلَيَّ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «ذَاكَ شَيْطَانٌ يُقَالُ لَهُ خِنْزَِبٌ، فَإِذَا أَحْسَسْتَهُ فَتَعَوَّذْ بِاللهِ مِنْهُ، وَاتْفُلْ عَلَى يَسَارِكَ ثَلَاثًا»، قَالَ: فَفَعَلْتُ ذَلِكَ فَأَذْهَبَهُ اللهُ عَنِّي.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2203]
المزيــد ...
Daga usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi -:
Lallai ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah, lallai haƙiƙa Shaiɗan ya shiga tsakanina da sallata da kuma karatuna, yana rikitar da ni, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku", sai ya ce: Sai na aikata hakan sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2203]
Usman ɗan Abul Aas - Allah Ya yarda da shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa Shaiɗan haƙiƙa ya shiga tsakanina da sallata ya hanani khushu'i a cikinta, ya cakuɗa min karatuna ya sa ni kokwanto a cikinta, Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Wannan Shaiɗan ne ana ce masa Khinzab, idan ka ka sami hakan, kuma ka ji shi ka nemi mafaka a wurin Allah, ka nemi tsarin Allah daga gare Shi, ka yi tofi a hagunka tare da yawu kaɗan sau uku, Usman ya ce: Sai na aikata abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya umarce ni da shi, sai Allah Ya tafiyar da shi daga gareni.