+ -

عن ابنِ عَبَّاسٍ رضي الله عنهما عن النبيِّ صلى الله عليه وسلم قال:
«أُمِرْتُ أَنْ أَسْجُدَ عَلَى سَبْعَةِ أَعْظُمٍ: عَلَى الْجَبْهَةِ وَأَشَارَ بِيَدِهِ عَلَى أَنْفِهِ، وَالْيَدَيْنِ، وَالرُّكْبَتَيْنِ، وَأَطْرَافِ الْقَدَمَيْنِ، وَلَا نَكْفِتَ الثِّيَابَ وَالشَّعَرَ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 812]
المزيــد ...

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai: Akan goshi sai ya yi nuni da hannunsa akan hancinsa, da hannaye, da gwiwoyi, da gefunan diga-digai, kuma kada ka tufke tufafi ko gashi".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 812]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa Allah Ya umarce shi a yayin sallah ya yi sujjada akan gabbai bakwai na jiki; su ne:
Na farko: Goshi: Shi ne: Fatar fuska a saman hanci da idanuwa, Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni zuwa hancinsa, yana mai bayyana cewa goshi da hanci gaba daya ce daga bakwan, da kuma karfafa cewa mai sujjada yana shafar kasa da hancinsa.
Gaba ta biyu da ta uku: Hannaye.
Ta hudu da ta biyar: Gwiwoyi.
ta shida da ta bakwai: 'Yan yatsun diga-digai.
Kuma ya umarcemu kada mu daure gashin mu, ko mu tattaro tufafinmu sashinsu akan sashi a yayin sujjada akan kasa dan karesu; kai ya sake su har su sauka a kasa, sai ka yi sujjada tare da gabbai.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wajabcin yin sujjada a cikin sallah akan gabbai bakwai.
  2. Karhancin tattaro tufafi da gashi a cikin sallah.
  3. Yana wajaba akan mai sallah ya natsu a cikin sallarsa, hakan ya sanya gabban sujjada guda bakwai akan kasa, ya tabbata akansu har ya zo da zikirin da aka shara'anta.
  4. Hani daga kame gashi (wannan) ya kebanci maza banda mata; domin cewa mace a cikin sallah abar umarta ce da sutaurtawa.