عن أَنَس بن مالك -رضي الله عنه- عَنْ النَّبِيِّ -صلى الله عليه وسلم- قَالَ: «اعْتَدِلُوا في السجود، ولا يَبْسُطْ أحدكم ذِرَاعَيْهِ انْبِسَاطَ الكلب».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nas
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Annabi tsira da aminci yayi umarni da a daidaita cikin sujjada, ta yadda mai yin salla zai kasance cikin kyakkyawar kama a lokacin sujjada, ta yadda zai sa tafukansa a kasa, ya daga zirao'insa ya nesanta su da d kuibukansa, saboda wannan yanayin shi ne alamar karsashi dakwadayi wadanda ake nema a cikin salla, kuma irin wannan yanayin kan bada dama ga ko wace gaba ta sami nata rabon na ibada, an yi hani ga shimfida hannaye a cikin sujjada, don yana jawo lalaci da kosawa, kuma yinsa yin kama da kare ne, wanda bai dace ga mai yin salla ba.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin
Donate