عَنِ الْبَرَاءِ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِذَا سَجَدْتَ، فَضَعْ كَفَّيْكَ وَارْفَعْ مِرْفَقَيْكَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 494]
المزيــد ...
Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -:
"Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 494]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana halin hannaye a cikin sujjadar sallah, hakan da ya tabbatar da tafukansa a ƙasa kuma ya ɗora yatsun a ɗunƙule a fuskantar alƙibla, kuma gwiwowin hannaye - sune mararrabar zira'i da damutse - a ɗage daga taɓ ƙasa kuma a buɗe daga sasanni.