+ -

عن ابن عباس رضي الله عنهما:
كان النبي صلى الله عليه وسلم يقول بين السجدتين: «اللَّهمَّ اغْفِرْ لي، وارْحَمْنِي، وعافِني، واهْدِني، وارزقْنِي».

[حسن بشواهده] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 850]
المزيــد ...

Daga Ɗan Abbas Allah Ya yarda da su:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.

- - [سنن أبي داود - 850]

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana yin Addu’a tsakanin sujjada biyu a Sallarsa, da waɗannan addu’o’in biyar, wacce Musulmi yake da matuƙar buƙatar su, kuma sun ƙunshi alheran duniya da lahira, kamar neman gafara, da ɓoye zunubi, da kuma yafe su, da malalo rahama da waraka daga shubuhohi da abubuwan sha’awe-sha’awe da rashin lafiya da cututtuka , da kuma roƙon Allah samun shiriya a kan gaskiya da kuma tabbata a kanta, da arziki na imani da ilimi da aiki na ƙwarai da kuma dukiya ta halal mai daɗi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Shar’antuwar wannan Addu’ar a zaman dake tsakanin sujjada biyu.
  2. Falalar wannan Addu’ar saboda abin da ta ƙunsa na alheran duniya da lahira.