kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Dan Zubair ya kasance yana cewa a bayan kowacce Sallah idan ya yi sallama: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, Shi kaɗai Ya ke ba shi da abokin tarayya, mulki na Sa ne, kuma godiya ta Sa ce, kuma Shi mai iko ne a kan komai. Ba dabara ba ƙarfi sai da Allah, babu abin bauta da gaskiya sai Allah, ba ma bautawa kowa sai Shi, Shi Ya ke da ni’ima da falala, Shi ke da kyawawan yabo, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, muna masu tsarkake addini gare shi, ko da kafirai sun ƙi. Ya kuma ce:@ Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗinsu bayan kowacce sallah.
عربي Turanci urdu
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni.
عربي Turanci urdu
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya sallame daga sallah yana neman gafara sau uku, ya kuma ce:@ Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci* . Walid ya ce: Na cewa Awza’i: Ya neman gafarar yake? Ya ce: Za ka ce ne: Ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah,
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "@Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)*". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da aminci su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya yi kabbara a sallah, sai ya yi shiru ɗan wani lokaci gabanin fara karatu, sai na ce: Ya manzon Allah, fansarka baba na da Baba ta, kana ganin shirun da kake yi tsakanin kabbara da karatu, me kake cewa? ya ce: Ina cewa: @Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta*, Ya Allah Ka tsaftace ni daga zunubaina kamar yadda ake tsaftace farar tufa daga datti. Ya Allah Ka wanke ni daga zunubai na da ruwan ƙanƙara kuma mai tsananin sanyi".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Na rasa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare a shinfiɗa sai na lalube shi sai hannuna ya faɗa akan cikin diga-digansa alhali shi yana cikin masallaci alhali su suna a kafe, alhali shi yana cewa: @"Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Masu biyewa juna mai fadinsu ba ya tabewa - ko mai aikata su - a bayan kowacce sallar farilla, Tasbihi talatin da uku, da Tahmidi talatin da uku, da Kabbara talatin da hudu".
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
"Wanda ya karanta Ayatul kursiyyi a bayan kowacce sallar farilla to babu abinda zai hana shi shiga aljanna sai mutuwa".
عربي Turanci urdu
Sunyi Gaskiya, lallai su ana yi musu Azaba Azabar da Dabbobi suke ji baki xayansu
عربي Turanci urdu
:
عربي Turanci urdu
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla*: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".
عربي Turanci urdu
Ya Ubangijin jibrila da Mika'ila, da isarafilu, wanada ya halicci sammai da Qasa, wanda ya ke masanin gaibu da fili, kai ne wanda kake yin hukunci a tsakanin bayinka cikin abunda suka sabawa a cikinsa, ka shiryar da ni cikin abunda suka sava a cikinsa na gaskiya da ikonka, lallai kai ne Mai shiryar da wanda ka so zuwa tafarki madaidaici
عربي Turanci urdu
"Manzo tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi ya koyar da ni tahiya.hannu na na cikin hannayensa, kamar yadda yake koyar da ni Surar daga Alqur'ani"
عربي Turanci urdu
: : :
عربي Turanci urdu