عن أبي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قال: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم يدعو: اللَّهُمَّ إني أعوذ بك من عذاب القبر، وعذاب النار، ومن فتنة الْمَحْيَا وَالْمَمَاتِ، ومن فتنة الْمَسِيحِ الدَّجَّالِ». وفي لفظ لمسلم: «إذا تَشَهَّدَ أحدكم فَلْيَسْتَعِذْ بالله من أَرْبَعٍ، يقول: اللهُمَّ إني أعوذ بك من عذاب جَهَنَّم...». ثم ذكر نحوه.
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi yace: "Manzo ya kasance yana yin addu'a: Ya Ubangiji na Ina neman tsarinka daga azabar kabari, da kuma azabar wuta, daga fitinar rayuwa da mutuwa, daga fitinar Almassih Dajja". A wani lafazin na Muslim" "Idan dayanku yayi tahiya to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu, yace: Ya Ubangiji na Ina neman tsarinka daga azabar Jahannama..." sannan ya ambaci makamanciyarta.
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Annabi -tsira da aminci- ya nemi tsari daga abu hudu, kuma ya umarce mu da mu nemi tsarin Allah daga wadannan abubuwa hudu a cikin tahiyarmu ta salla, azabar kabari, azabar wuta, sha'awoyin duniya da shubuhohinta, fitinar mutuwa, neman tsari daga garesu sabo da hatsarinsu, fitinar kabari, wanda shi ne dalilin azabarsa, da fitinar rayuwa fitinar shaidanu masu bayyana ga mutane kamar suna tare da gaskiya alhali kuwa sabani hakanne, mafi girman fitinar cikinsu shi ne Dujal wanda bayyanarsa ta tabbata a karshen zamani don haka Annabi ya ambace shi daban.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Swahili Yaran Tamili Yaran Tailand bushtu Asami السويدية الأمهرية
Manufofin Fassarorin