عن ثَوْبَانَ رضي الله عنه قال:
كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا انْصَرَفَ مِنْ صَلَاتِهِ اسْتَغْفَرَ ثَلَاثًا، وَقَالَ: «اللَّهُمَّ أَنْتَ السَّلَامُ، وَمِنْكَ السَّلَامُ، تَبَارَكْتَ ذَا الْجَلَالِ وَالْإِكْرَامِ»، قَالَ الْوَلِيدُ: فَقُلْتُ لِلْأَوْزَاعِيِّ: كَيْفَ الْاسْتِغْفَارُ؟ قَالَ: تَقُولُ: أَسْتَغْفِرُ اللهَ، أَسْتَغْفِرُ اللهَ.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 591]
المزيــد ...
Daga Sauban, Allah Ya yarda da shi:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya sallame daga sallah yana neman gafara sau uku, ya kuma ce: Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareka yake, Ka ɗaukaka ya ma’abocin girma da karamci . Walid ya ce: Na cewa Awza’i: Ya neman gafarar yake? Ya ce: Za ka ce ne:
Ina neman gafarar Allah, ina neman gafarar Allah,
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 591]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa idan ya kammala sallarsa; Ina neman gafar Allah, Ina neman gafarar Allah, Ina neman gafarar Allah.
Sannan sai ya girmama Ubangijinsa, ya ce: "Ya Ubangiji Kai ne aminci, kuma aminci daga gareKa yake, Ka girmama ya ma’abocin girma da karamci".
Shi Allah tsarkakke ne, kuma cikakke ne a siffofinsa, kuma Ya tsarkaka daga barin kowanne aibu da tawaya, kuma ka nemi waraka daga dukkan sharri duniya da lahira daga wajenSa ba daga wani ba, Shi Allah alheranSa sun yawaita a duniya da lahira, Ma’abocin girma da kyautatawa ne.