عَنْ وَائِل بن حُجرٍ رضي الله عنه قَالَ:
صَلَّيْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَكَانَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ»، وَعَنْ شِمَالِهِ: «السَّلَامُ عَلَيْكُمْ وَرَحْمَةُ اللَّهِ».  
                        
[حسن] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 997]
                        
 المزيــد ... 
                    
Daga Wa'il ɗan Hujur - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
 "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: 
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
"Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah". 
                                                     
                                                                                                    
[Hasan ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 997]                                            
                        Annabin - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin ya juya daga sallarsa zai yi sallama a damansa da hagunsa shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren dama, tare da faɗinsa: 
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
(Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa), kuma yana yin sallama a hagunsa, shi ne ya juyar da fuskarsa ɓangaren hagu, tare da faɗinsa: 
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh.
(Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah).