kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

An umarceni in yi sujjada akan gabbai bakwai
عربي Turanci urdu
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangiji ka gafarta min, ka yi min rahama, ka ba ni lafiya, ka shiryar da ni, ka azurta ni
عربي Turanci urdu
Annabi tsira da amincin Allah -ya kasance yana daga hannayensa daura da kafadunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi ruku'u, da kuma yayin da yake dagowa daga ruku'u.
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sanar dani Tahiya, tafukana tsakanin tafukansa, kamar yadda yake sanar dani sura daga Alkur’ani
عربي Turanci urdu
Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nasa.
عربي Turanci urdu
Idan liman ya ce Ameen kuma ku ce Ameen ,domin duk wanda Ameen dinsa ta dace da ta Mala'iku to an gafarta masa abunda ya gabata na zunubansa.
عربي Turanci urdu
Idan kayi Sujada to ka sanya tafin Hannayenka kuma ka xaga Dantsanka
عربي Turanci urdu
Idan Xayanku zai yi Sujada kada ya Durkusa kamar yadda Raqumi yake Durqusawa, ya fara sanya Hannayensakafin Guiwoyinsa
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Ibn umar ya kasance yana sanya Hannayensa kafin guiwoyinsa, kuma ya ce: Manzon Allah SAW ya kasance yana yin hakan
عربي Turanci urdu
Nayi Sallah tare da Manzon Allah SAW ya kasance yana yin Sallama a damansa da cewa: Amincin Allah a gare ku da rahamar Allah da Albarkatunsa, kuma a Hagunsa: Amincin Allah a gare ku da rahamar Allah
عربي Turanci urdu
ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata
عربي Turanci urdu
Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara
عربي Turanci urdu
na rantse da wanda raina yake a hannunSa lallai ni ne mafi kusancinku kamanceceniya da sallar manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wannan ita ce sallarsa har ya bar duniya
عربي Turanci urdu
Mafi munin mutane sata shi ne wanda yake satar sallarsa" sai ya ce: Ta yaya zai saci sallarsa? sai ya ce: "Ya zamo ba ya cika ruku'unta, ba ya cika sujjadarta
عربي Turanci urdu
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan ya ɗago bayansa daga ruku'u sai ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa
عربي Turanci urdu
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a tsakanin sujjada biyu; "Ya Ubangijina Ka gafarta mini, ya Ubangijina Ka gafarta min'
عربي Turanci urdu
Wannan wani Sahiɗan ne ana ce masa khinzab, idan ka ji shi ka nemi tsarin Allah daga gare shi, ka yi tofi a hagunka sau uku
عربي Turanci urdu
Manzon Allah ya kasance in zaiyi salla sai yayi kabbara yayin da yake mikewa, sannan kuma yana yin kabbara yayin da yake yin ruku'u, sannan yana cewa: Allah ya ji mai gode masa, yayin da yake dago bayansa daga raka'a
عربي Turanci urdu
Na lura da sallar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- sai na sami tsayuwarsa, da ruku'unsa, da daidaitonsa bayan ruku'u,da sujjadarsa, da zamansa tsakanin sujjada biyu, da zamansa tsakanin sallama da juyawa: kusan daidai da daidai.
عربي Turanci urdu
Cewa Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-ya shiga Masallaci,sai wani Mutum ya shigo yayi Salla,sannan yazo yayi sallama ga Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-sai yace:koma kayi Salla,domin cewa kai baka yi Salla ba.sai ya koma yayi Salla kamar yadda yayi Sallar,sannan yazo yayi sallama ga-Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi- sai yace:koma kayi Salla,domin cewa kai bakayi Salla ba-sau Uku-sannan yace:Na rantse da wanda ya aikoka da Gaskiya bazan iya yin wacce tafita ba,to ka sanar dani,sai yace:Idan ka nufi yin Salla kayi Kabbara,sannan ka karanta abinda ya saukaka daga Al-Kur'ani,sannan kayi Ruku'u har sai ka daidaita kana mai Ruku'u,sannan ka dago har ka daidaita kana mai tsayuwa,sannan kayi Sajada har sai ka nutsu kana mai sajada,sannan ka dago har sai ka nutsu kana mai zama.kayi haka acikin kowace Sallarka.
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Annabi ya kasance yana Sallah kuma ya na dauke da Umama Yar Zainab Yar Annabi
عربي Turanci urdu
Na yi salla tare da Abu Bakr, Omar da Othman, kuma ban ji ɗayansu ya karanta "Da sunan Allah ba, Mai jin ƙai, Mai jin ƙai."
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Annabi ya aika Wani Mutum a wani yaki sai ya kasane yana" karantawa abokansa in yana jansu Sallah, Sai yake cika karatunsa da: Kulhuwa.
عربي Turanci urdu
Ni da Imran bn Husayn mun yi salla a bayan Ali bin Abi Dalib, don haka idan ya yi sujjada, sai ya ce takbire, idan ya daga kansa sai ya ce takbire, idan kuma ya tashi daga rakaoin biyu, zai ce takbire.
عربي Turanci urdu
Na ji Annabi -tsira da amincin Allah- yana karanta Suratuddur a Sallar Magariba.
عربي Turanci urdu
Lallai ni wallahi zan yi muku sallah , amma ba sallar nake nufi ba, ina yin sallah ne yadda naga manzon Allah mai tsira da aminchi yake yin sallah.
عربي Turanci urdu
Naga Manzon Allah SAW yana yiwa Mutane limanci kuma umama Bint Abi Al-as ita ce Xiyar Zainab Xiyar Manzon Allah SAW tana kan kafaxarsa, idan yayi Ruku'u sai ya Ajiye ta, kuma idan ya Xago daga Sujada sai ya Mayar da ita
عربي Turanci urdu
Ku Kashe Baqaqe biyu ko a cikin Sallah ne: Macijiya da kuma Kunama
عربي Turanci urdu
Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana bude salla da yin kabbara, da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, baya kuma mikar da shi saidai tsaka tsaki
عربي Turanci urdu
Nayi Sallah tare da Manzon Allah SAW ya sanysa Hannunsa na Dama kan Hannunsa na Hagu akan Qirjinsa
عربي Turanci urdu
Abin da na yi a bayan wani kamar addu’ar Manzon Allah ne, amincin Allah ya tabbata a gare shi, daga haka-da-haka.
عربي Turanci urdu
Cewa Manzon Allah SAw ya kasance ian ya yayi Ruku'u yana rarraba 'Yanyatsunsa kuma idan yayi Sujada sai ya haxe su
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah SAW idan ya kasanc a Wuturin Sallarsa baya tashi har sai ya daidaita a zaune
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-qunuti Wata xaya bayan Ruku'u yana Addu'a ga wasu Mutane daga Qabilar Bani Sulaim
عربي Turanci urdu
Lallai cewa Manzon Allah SAW ya kasance baya Al-qunuti sai in zai Addu'a ga wasu Mutane, ko yayi Addu'a kan wasu Mutane
عربي Turanci urdu
Ya Babana lallai kai kayi Sallah bayan Manzon Allah SAW da kuma Abubakar da Umar da Usman da Ali a nan Kufa, wajen Shekara Biyar, shin sun kasance suna Al-qunuti a Asuba? sai ya ce: Ai Xana Wannan fararre ne
عربي Turanci urdu
Manzon Allah SAW ya kasance idan ta zauna yana Addu'a, kuma yana sanya Hannunsa na dama akan cinyarsa ta dama kuma Hannunsa na Hagu kan cinyarsa ta Hagu, kuma yana nuni da Xanyatsansa na nuni, kuma yana sanya Babban Xanyatsansa a kan na tsakiya, kuma yana xora tafin Hannunsa na Hagu kan kan Guiwarsa
عربي Turanci urdu
Allah ka kuvutar da Ayyash Bn Abi rabi'a Ya Ubanhiji ka kuvutar da Sakamah Bn Hisham Ya Ubangiji ka kuvutar da Al-walid Bn Alwalid, Ya Ubangiji ka kuvutar da raunanan Muminai, Ya Ubangiji ka tsananta Kamunka ga Mudhar, Allah ka sanya musu yinwa kamar Shekarun Annabi Yusuf
عربي Turanci urdu
Manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana bude salla da yin kabbara, da karatu, da fadar Alhamdu lillahi rabbil aalamina, ya kasance idan yayi ruku`u baya dago kansa, baya kuma mikar da shi saidai tsaka tsaki
عربي Turanci urdu
Cewa Manzon Allah SAW ya kasance idan zai kabbara yana xaga Hannayensa har sai sunkai daidai Kunnuwansa, kuma idan yayi ruku'u yana xaga Hannayensa har sukai daidai kunnuwansa
عربي Turanci urdu