عن أَبِي حَازِمِ بْن دِينَارٍ:
أَنَّ رِجَالًا أَتَوْا سَهْلَ بْنَ سَعْدٍ السَّاعِدِيَّ، وَقَدِ امْتَرَوْا فِي الْمِنْبَرِ مِمَّ عُودُهُ، فَسَأَلُوهُ عَنْ ذَلِكَ، فَقَالَ: وَاللهِ إِنِّي لَأَعْرِفُ مِمَّا هُوَ، وَلَقَدْ رَأَيْتُهُ أَوَّلَ يَوْمٍ وُضِعَ، وَأَوَّلَ يَوْمٍ جَلَسَ عَلَيْهِ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، أَرْسَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِلَى فُلَانَةَ -امْرَأَةٍ من الأنصار قَدْ سَمَّاهَا سَهْلٌ-: «مُرِي غُلَامَكِ النَّجَّارَ أَنْ يَعْمَلَ لِي أَعْوَادًا أَجْلِسُ عَلَيْهِنَّ إِذَا كَلَّمْتُ النَّاسَ»، فَأَمَرَتْهُ فَعَمِلَهَا مِنْ طَرْفَاءِ الْغَابَةِ، ثُمَّ جَاءَ بِهَا، فَأَرْسَلَتْ إِلَى رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَأَمَرَ بِهَا فَوُضِعَتْ هَاهُنَا، ثُمَّ رَأَيْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ صَلَّى عَلَيْهَا وَكَبَّرَ وَهُوَ عَلَيْهَا، ثُمَّ رَكَعَ وَهُوَ عَلَيْهَا، ثُمَّ نَزَلَ الْقَهْقَرَى، فَسَجَدَ فِي أَصْلِ الْمِنْبَرِ ثُمَّ عَادَ، فَلَمَّا فَرَغَ أَقْبَلَ عَلَى النَّاسِ فَقَالَ: «أَيُّهَا النَّاسُ، إِنَّمَا صَنَعْتُ هَذَا لِتَأْتَمُّوا وَلِتَعَلَّمُوا صَلَاتِي».

[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abu Hazim Dan Dinar
Lallai wasu mutane sun zo wa Sahlu ɗan Sa'ad Al-sa'idiy alhali sun yi musu a sha'anin minbarin (Manzon Allah) katakwayensa na mene ne, sai suka tambaye shi game da hakan, sai ya ce: Na rantse da Allah ni na san na mene ne su, haƙiƙa na gan shi a farkon ranar da aka ajiye shi, da kuma farkon ranar da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fara zama a kansa, Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wance - wata mace daga Mutanen Madina -Sahlu ya ambace ta -; "Ki umarci yaronki kafinta ya haɗa min katakwaa da zan zauna a kansu idan zanyiwa mutane magana". Sai ta umarce shi sai ya yisu daga bishiyoyin daji, sannan ya zo da su, sai ta aika zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni aka ajiyesu a nan, sannan na ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansu ya yi kabbara alhali yana kansu, sannan ya yi ruku'u alahali yana kansu, sannan ya sauko da baya, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, yayin da ya gama sai ya fuskanci mutane sai ya ce: "ya ku mutane, kawai na aikata haka ne don ku yi koyi da ni, kuma ku san sallata".

Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Wasu mutane sun zo wa ɗaya daga sahabbai suna tambayarsa game da minbarin Annabi wanda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya riƙeshi: Da me aka yi shi? Haƙiƙa sun yi jayayya a hakan, sai ya ambata musu cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aika zuwa ga wata mata daga Mutanen Madina tana da wani yaro kafinta, sai ya ce da ita: Ki umarci yaronki ya yi min minbarin da zan zauna a kansa lokacin da zan yi wa mutane magana, sai matar ta amsa, ta umarci yaronta ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - minbari na bishiyar Ɗarfa'u, lokacin da ya gama sai matar ta aika da munbarin zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, sai ya yi umarni da shi sai aka ajiye shi a wurinsa a masallaci, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi sallah a kansa ya yi kabbara alhali yana kansa, sannan ya yi ruku'u alhali yana kansa, sannan ya sauka yana tafiya ta baya, ba tare da ya juyo da fuskarsa ba zuwa ta baya ba, sai ya yi sujjada a asalin minbarin sannan ya dawo, lokacin da ya gama sallar sai ya fuskanci mutane, ya ce: ya ku mutane, kaɗai na aikata haka ne don ku yi koyi kuma ku san sallata.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. An so riƙon minbari da hawan mai huɗuba a kansa, fa'idarsa ita ce isar wa da kuma jiyarwa.
  2. Halaccin sallah a kan minbari don koyarwa, da halaccin ɗaukakar liman ga mamu don buƙata.
  3. Halaccin neman taimako da masu sana'o'i a buƙatun musulmai.
  4. Halaccin motsi kaɗan a sallah don buƙata.
  5. Halaccin kallon mamu zuwa limaminsa a sallah; don ya koya daga gare shi , kuma hakan ba ya kore khushu'i.