+ -

عَنْ ‌حِطَّانَ بْنِ عَبْدِ اللهِ الرَّقَاشِيِّ قَالَ: صَلَّيْتُ مَعَ ‌أَبِي مُوسَى الْأَشْعَرِيِّ صَلَاةً، فَلَمَّا كَانَ عِنْدَ الْقَعْدَةِ قَالَ رَجُلٌ مِنَ الْقَوْمِ: أُقِرَّتِ الصَّلَاةُ بِالْبِرِّ وَالزَّكَاةِ، قَالَ: فَلَمَّا قَضَى أَبُو مُوسَى الصَّلَاةَ وَسَلَّمَ انْصَرَفَ فَقَالَ: أَيُّكُمُ الْقَائِلُ كَلِمَةَ كَذَا وَكَذَا؟ قَالَ: فَأَرَمَّ الْقَوْمُ، ثُمَّ قَالَ: أَيُّكُمُ الْقَائِلُ كَلِمَةَ كَذَا وَكَذَا؟ فَأَرَمَّ الْقَوْمُ، فَقَالَ: لَعَلَّكَ يَا حِطَّانُ قُلْتَهَا؟ قَالَ: مَا قُلْتُهَا، وَلَقَدْ رَهِبْتُ أَنْ تَبْكَعَنِي بِهَا، فَقَالَ رَجُلٌ مِنَ الْقَوْمِ: أَنَا قُلْتُهَا، وَلَمْ أُرِدْ بِهَا إِلَّا الْخَيْرَ، فَقَالَ أَبُو مُوسَى: أَمَا تَعْلَمُونَ كَيْفَ تَقُولُونَ فِي صَلَاتِكُمْ؟ إِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَطَبَنَا فَبَيَّنَ لَنَا سُنَّتَنَا وَعَلَّمَنَا صَلَاتَنَا، فَقَالَ:
«إِذَا صَلَّيْتُمْ فَأَقِيمُوا صُفُوفَكُمْ، ثُمَّ لِيَؤُمَّكُمْ أَحَدُكُمْ فَإِذَا كَبَّرَ فَكَبِّرُوا، وَإِذْ قَالَ: {غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلا الضَّالِّينَ} [الفاتحة: 7]، فَقُولُوا: آمِينَ، يُجِبْكُمُ اللهُ، فَإِذَا كَبَّرَ وَرَكَعَ فَكَبِّرُوا وَارْكَعُوا، فَإِنَّ الْإِمَامَ يَرْكَعُ قَبْلَكُمْ، وَيَرْفَعُ قَبْلَكُمْ»، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَتِلْكَ بِتِلْكَ، وَإِذَا قَالَ: سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، فَقُولُوا: اللَّهُمَّ رَبَّنَا لَكَ الْحَمْدُ، يَسْمَعِ اللهُ لَكُمْ، فَإِنَّ اللهَ تَبَارَكَ وَتَعَالَى قَالَ عَلَى لِسَانِ نَبِيِّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: سَمِعَ اللهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، وَإِذَا كَبَّرَ وَسَجَدَ فَكَبِّرُوا وَاسْجُدُوا، فَإِنَّ الْإِمَامَ يَسْجُدُ قَبْلَكُمْ وَيَرْفَعُ قَبْلَكُمْ»، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «فَتِلْكَ بِتِلْكَ، وَإِذَا كَانَ عِنْدَ الْقَعْدَةِ فَلْيَكُنْ مِنْ أَوَّلِ قَوْلِ أَحَدِكُمُ: التَّحِيَّاتُ الطَّيِّبَاتُ الصَّلَوَاتُ لِلهِ، السَّلَامُ عَلَيْكَ أَيُّهَا النَّبِيُّ وَرَحْمَةُ اللهِ وَبَرَكَاتُهُ، السَّلَامُ عَلَيْنَا وَعَلَى عِبَادِ اللهِ الصَّالِحِينَ، أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَأَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 404]
المزيــد ...

Daga Hiɗɗan ɗan Abdullahi Al-Raƙashi ya ce: Na sallaci wata sallah tare da Abu Musa Al-Assh'ari, a lokacin zama sai wani mutum daga mutane ya ce: An haɗa sallah da aikin alheri da kuma zakka, ya ce: Lokacin da Abu Musa ya gama sallar ya yi sallama, sai ya juya ya ce: Waye mai faɗin kalmar kaza da kaza a cikinku? ya ce: Sai mutane suka yi shiru, sannan ya ce: Waye ya faɗi kalmar kaza da kaza a cikinku? sai mutane suka yi shiru, sai ya ce: Wataƙila kai Hiɗɗanu kai ka faɗeta? sai ya ce: Ban faɗeta ba, haƙiƙa na ji tsoron kada ka zargeni da ita, sai wani mutum daga mutanen ya ce: Ni na faɗeta, kuma ban nufi komai da ita ba sai alheri, sai Abu Musa ya ce: Shin kun san me zaku fada a sallarku? lallai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi mana huɗuba sai ya bayyana mana sunnonimmu, ya kuma sanar da mu sallolinmu.
"Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗayanku ya yi muku limanci, idan ya yi kabbara sai ku yi kabbara, idan ya ce: {Ba waɗanda ka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba} [Al-Fatiha: 7], sai ku ce: Ameen, Allah zai amsa muku, idan ya yi kabbara ya yi ruku'u, sai ku yi kabbara ku yi ruku'u, domin cewa liman yana yin ruku'u ne kafinku, kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sai ku ce: Ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa, Allah Zai jiye muku (wato Zai amsa); domin cewa Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya faɗa a kan harshen AnnabinSa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, idan ya yi kabbara ya yi sujjada sai ku yi kabbara sai ku yi sujjada, domin cewa liman yana yin sujjada ne kafinku kuma yana ɗagowa ne kafinku", sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Waccan da waccan, idan an zo wurin zama; to, farkon abin da ɗayanku zai faɗa (shi ne): gaisuwa ta tabbata ga Allah tsarkakan salloli sun tabbata ga Allah, aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da bayin Allah nagari, ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ina shaida cewa (Annabi) muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 404]

Bayani

Sahabi Abu Musa Al-Ash'ariy - Allah Ya yarda da shi - ya yi wata sallah, alokacin da ya yi zaman da a cikinsa akwai tahiya, sai wani mutum daga masallata a bayansa ya ce: An haɗa sallah a cikin Alkur’ani da aikin alheri da kuma zakka, lokacin da Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya gama sallar sai ya fuskanci mamu, sai ya tambayesu: Waye a cikinku ya faɗi kalmar: An haɗa sallah da aikin alheri da zakka a cikin Alkur’ani ?! sai mutanen suka yi shiru, wani daga cikinsu bai yi magana ba, sai ya maimaita musu tambayar karo na gaba, yayin da babu wanda ya amsa masa, sai Abu Musa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wata ƙila kai ya Hiɗɗan kai ka faɗeta! don ƙarfin halinsa da kuma kusancinsa gareshi, da dangantakarsa da shi ta yadda ba zai cutar da shi ba a tuhumarsa, kuma don ya sanya mai maganar na haƙiƙa zuwa tabbatarwa, sai Hiɗɗan ya kore hakan, sai ya ce: Haƙiƙa na ji tsoron za ka zargeni saboda zaton cewa ni na faɗeta; a nan sai wani mutum daga mutanen ya ce: Ni na faɗeta, kuma ban nufi komai da ita ba sai alheri, sai Abu Musa ya ce yana mai sanar da shi; Shin kun san ya za ku ce a sallarku?! hakan nuna ƙyama ne da ɓangarensa, sannan a ƙarshe Abu Musa ya sanar da cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi musu huɗuba wata rana, sai ya bayyana musu shari'o'insu, ya kuma sanar da su sallarsu, sai (Annabi) tsira da amin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
Idan za ku yi sallah, to, ku daidaita sahunku, sannan ɗaya daga cikinku ya yi muku limanci, idan liman ya yi kabbarar harama, sai ku yi kabbara irinsa, idan ya karanta fatiha ya kai { Ba waɗanda aka yi fushi da su ba, ba kuma ɓatattu ba} [Al-Fatiha: 7], sai ku ce: Ameen; idan kun aikata hakan Allah Zai amsa muku addu'arku, idan ya yi kabbara ya yi ruku'u sai ku yi kabbara ku yi ruku'u; domin cewa liman yana ruku'u ne kafinku kuma yana ɗagowa kafinku, kada ku rigaye shi; domin a lokacin liman ya rigayeku a gabatowa zuwa ruku'u; to, za ta gyara muku da jinkirinku a ruku'u bayan ɗagowarsa a lokacin, to, waccan lokacin da waccan lokacin, sai gwargwadon ruku'inku ya zama kamar gwargwadon ruku'insa, idan liman ya ce: Allah ya ji wanda ya gode maSa, sai ku ce: ya Allah Ubangijinmu godiya ta tabbata gareKa, idan masallata suka faɗi hakan, to, Allah - tsarki ya tabbatar maSa - Yana jin addu'arsu da kuma maganarsu; domin cewa Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - ya faɗa a kan harshen AnnabinSa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, sannan idan ya yi kabbara ya yi sujjada, to, ya wajaba a kan mamu su yi kabbara su yi sujjada, domin cewa liman yanayin sujjada ne kafinsu, kuma yana ɗagowa ne kafinsu, to, waccan lokacin da waccan lokacin, kuma gwargwadon sujjadar mamu ya zama kamar gwargwadan sujjadar liman ne, idan ya kasance a lokacin zama domin tahiya ne, to, farkon faɗin mai sallah ya zama: "Gaisuwa da tsarkakan salloli sun tabbata ga Allah" mulki da wanzuwa da girma dukkaninsu ababen cancanta ne ga Allah - Maɗaukakin sarki -, haka nan salloli biyar dukkaninsu na Allah ne, "Aminci ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar Allah da albarkacinSa, aminci ya tabbata agaremu da kuma bayin Allah na gari", to, ku roƙi Allah kuɓuta daga dukkanin aibi da tawaya da ɓarna; kuma muna keɓantar Annabinmu Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - da sallama, sannan mu yi wa kawunanmu sallama, sannan mu yi sallama ga bayin Allah na gari masu tsayawa da abin da ya wajaba a kansu na haƙƙokin Allah da kuma haƙƙokin bayinSa, sannan mu shaida cewa babu abin bautawa da agsakiya sai Allah, kuma mu shaida cewa (Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Tagalog Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin siga daga sigogin tahiya.
  2. Ayyukan sallah da maganganunta babu makawa su zama daga abin da ya tabbata ne daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ba ya halatta ga wani ya ƙirƙiri wata magana ko wani aiki a cikinta wanda bai tabbata a sunna ba.
  3. Rashin halaccin rigayar liman da kuma jinkirtawa gare shi, abin da aka halatta ga mamu shi ne bin liman a cikin ayyukansa.
  4. Ambaton abin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a kai na himmantuwa wajen isarwa, da kuma sanar da al'ummarsa hukunce-hukuncen Addini.
  5. Liman shi ne (abin) koyi ga mamu, ba ya halatta gare shi ya rigaye shi a ayyukan sallah, ko ya gwama da shi, ko ya jinkirta akan sa, kawai ya zama tun farko koyi zai yi da shi bayan tabbatar da cewa ya shiga a aikin da yake nufin aikata shi, kuma sunna ita ce binsa (koyi da shi) a cikinsa.
  6. Shar’antuwar daidaita sahu a sallah.