عن عبد الله بن مَسْعُود رضي الله عنه قال: عَلَّمَنِي رسول الله صلى الله عليه وسلم التَّشَهُّد، كَفِّي بين كفيه، كما يُعَلِّمُنِي السورة من القرآن: التَّحِيَّاتُ للَّه، وَالصَّلَوَاتُ وَالطَّيِّبَاتُ، السلام عليك أيها النبي ورحمة الله وبركاته، السلام علينا وعلى عباد الله الصالحين، أشهد أن لا إله إلا الله وأشهد أن محمدا عبده ورسوله». وفي لفظ: «إذا قعد أحدكم في الصلاة فليقل: التحيات لله...» وذكره، وفيه: «فإنكم إذا فعلتم ذلك فقد سَلَّمْتُمْ على كل عبد صالح في السماء والأرض ...» وفيه: « ... فَلْيَتَخَيَّرْ من المسألة ما شاء».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Mas'ud Allah ya yarda da shi- yace:"Manzo tsira da amincin Alla su tabbata a gare shi ya koyar da ni tahiya.hannu na na cikin hannayensa,kamar yadda yake koyar da ni Surar daga Alqur'ani:Dukkanin gaisuwa ga Allah suke,hakanan addu'o'i da kyawawan ibadoji,aminci da rahamar Allah da albarkokin Allah sun tabbata gare ka ya kai wannan Annabi,aminci garema hakana ga bayinka na gari,Ina shedawa da cewa ba abin bautawa da gaskiya da cancanta sai Allah,kuma Ina shaida cewa lallai Annabi Muhammadu Bawansa ne kuma Manzonsa ne." Awani lafazin:"Idan dayanku ya zaman tahiyar salla sai yace: gaisuwoyi duka ga Allah suke..." ya ambata tahiyar,har yace:"lallai in kuka yi tahiya to kun gaida duk wani bawan Allah na gari na kasa da sama..."ya kuma cewa:"Sai ya yi addu'ar da yaso."
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Abdullahi Dan Mas'ud -Allah ya yarda da shi yana bamu labarin yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya masa tahiyar da ake fada a zaman farko da na biyu ga salla mai raka'a hudu da mai raka'a uku,da kuma zaman karshe ga salla mai raka'a biyu,da yadda Annabi ya damu da koya masa tahiya har ya sanya hannunsa a cikin hannunsa.Tahiya tana farawa da girmama Allah Madaukaki,girmamawa marar qaidi, kuma lallai shi ne ya cancanci ayi masa salla da sauran ibadoji,da kyawawan ayyuka da zantuka da siffofi.Bayan ya yabi Allah Madaukaki,sai ya bi da yiwa Annabi addu'ar neman aminci da kubuta daga duk wasu tauye-tauye,kuma ya rokar masa rahama da alheri,sannan ya rokawa kansa da wadanda suke nan mutane da mala'iku.Sannan ya game da adduarsa duukkan bayin Allah na gari,mutane da aljanu,mala'iku na sama dana kasa,wadanda suka wuce ,da masu zuwa,wannan yana daga dunkulallun kalmominsa -tsira da aminci su tabbata a gare shi-.Sannan ya shaida da shahada mai yanke cewar: Ba abin bauta da gaskiya sai Allah,kuma Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi-Manzonsa ne,Wannan shaida na da sifofi biyu:Sifa ta farko:ta sifantu da sifar bauta.Sifa ta biyu:Sifar risala watau sako.Duka sifofin sifofi ne na karamci da daukaka, sannan kuma kwai tsayuwa a tsaka tsaki, tsakanin ketare iyaka da gazawa.Sifofin tahiya sun zo da dama,amma wannan sifar ta Dan Mas'ud itace mafi shaara da daukaka,kuma ya halarta kayi wata sifar daga sifofin da suka inganta.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Swahili
Manufofin Fassarorin