عَن ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما:
أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَرْفَعُ يَدَيْهِ حَذْوَ مَنْكِبَيْهِ إِذَا افْتَتَحَ الصَّلَاةَ، وَإِذَا كَبَّرَ لِلرُّكُوعِ، وَإِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ مِنَ الرُّكُوعِ، رَفَعَهُمَا كَذَلِكَ أَيْضًا، وَقَالَ: «سَمِعَ اللَّهُ لِمَنْ حَمِدَهُ، رَبَّنَا وَلَكَ الحَمْدُ»، وَكَانَ لاَ يَفْعَلُ ذَلِكَ فِي السُّجُودِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 735]
المزيــد ...
Daga Ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -:
Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah, haka nan in zai yi kabbara dan ruku'u, haka idan kuma zai ɗago kansa daga ruku'u sai ya ɗagasu, kuma ya ce: "Allah Ya ji wanda ya gode maSa, ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gare ka, ya kasance ba ya yin haka a cikin sujjada.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 735]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya kasance yana ɗaga hannayensa agurare uku a sallah, daura da kafaɗa wanda shi ne: Matattarar ƙashin kafaɗa da damtse.
Guri na farko: Idan zai buɗe sallah yayin kabbarar harama.
Na biyu: Idan Zai yi kabbara dan ruku'u.
Na uku: Idan ya ɗago kansa daga ruku'u kuma ya ce: Allah Ya ji wanda ya gode maSa, Ya Ubangijinmu godiya ta tabbata gareka.
Ya kasance ba ya ɗaga hannayensa a lokacin fara sujjada, ko lokacin ɗagowa daga sujjada.