عن سالم بن أبي الجَعْدِ قال: قال رجل: ليتني صَلَّيتُ فاسترحْتُ، فكأنّهم عابُوا ذلك عليه، فقال: سمعتُ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«يا بلالُ، أقِمِ الصَّلاةَ، أرِحْنا بها».
[صحيح] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 4985]
المزيــد ...
Daga Salim ɗan Abulja'ad ya ce: Wani mutum ya ce: Ina ma dai na yi sallah in huta, kamar cewa su (sauran mutanen) sun aibata masa hakan, sai ya ce: Naji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Ya Bilai, ka yi iƙamar sallah, ka hutar da mu da ita".
[Ingantacce ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 4985]
Wani mutum daga sahabbai ya ce: Ina ma na yi sallah in huta, kai ka ce waɗanda ke gefensa sun aibata hakan gare shi , sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Ya kai Bilal! ka kira sallah ka yi iƙamarta; don mu samu hutu da ita; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma hutu ga rai da zuciya.