عن عمر بن الخطاب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«إِذَا قَالَ الْمُؤَذِّنُ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، فَقَالَ أَحَدُكُمُ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، ثُمَّ قَالَ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، ثُمَّ قَالَ: أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، قَالَ: أَشْهَدُ أَنَّ مُحَمَّدًا رَسُولُ اللهِ، ثُمَّ قَالَ: حَيَّ عَلَى الصَّلَاةِ، قَالَ: لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، ثُمَّ قَالَ: حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، قَالَ: لَا حَوْلَ وَلَا قُوَّةَ إِلَّا بِاللهِ، ثُمَّ قَالَ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، قَالَ: اللهُ أَكْبَرُ اللهُ أَكْبَرُ، ثُمَّ قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، قَالَ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ مِنْ قَلْبِهِ دَخَلَ الْجَنَّةَ».

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da a mincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan ladani ya ce: Allah ne mafi girma, Allah ne mafi girma, sai ɗayanku ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: Ina shaida wa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce; Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sannan ya ce; Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa sallah, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Ku yi gaggawa zuwa tsira, sai ya ce: Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, sannan ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sai ya ce: Allah ne mafi girma Allah ne mafi girma, sannan ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, sai ya ce: babu abin bautawa da gaskiya sai Allah daga zuciyarsa zai shiga aljanna".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Kiran sallah shi ne sanar da mutane shigowar lokacin sallah, kuma kalmomin kiran sallah kalmomi ne masu tattaro aƙidar imani.
A wannan Hadisin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana abin da aka shara'anta a yayin jin kiran sallah, shi ne mai ji ya faɗi irin abin da ladanin yake faɗa, idan ladani ya ce: "Allah ne mafi girma", mai ji ya ce: "Allah ne mafi girma", haka nan; sai dai a lokacin fadin ladani: "Ku yi gaggawa zuwa sallah", "Ku yi gaggawa zuwa tsira" sai mai ji ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah".
Kuma Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya bayyana cewa wanda ya maimaita tare da ladani yana mai tsarkake (niyya) daga zuciyarsa zai shiga aljanna.
Ma'anonin kalmar kiran sallah: "Allah ne mafi girma": Wato cewa Shi (Allah) - tsarki ya tabbatar maSa - Shi ne mafi girma mafi ɗaukaka mafi girma daga dukkan komai.
"Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah" wato babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
"Ina shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne": Wato ina tabbatarwa kuma ina shaidawa da harshena da zuciyata cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, Allah - Mai girma da ɗaukaka -Ya aiko shi , kuma yana wajaba a yi masa biyayya .
"Ku yi gaggawa zuwa sallah", wato ku zo zuwa sallah, da faɗin mai ji: "Babu dabara kuma babu karfi sai ga Allah", wato babu dabara a kuɓuta daga abubuwan da suke hana biyayya, babu ƙarfi a kan aikatasu, kuma babu iko a kan kowanne abu daga abubuwa sai dace daga Allah - Maɗaukakin sarki -.
"Ku yi gaggawa zuwa tsira", wato ku zo zuwa sababin tsira, shi ne rabauta da aljanna da tsira daga wuta.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar amsawa ladani da irin abin da yake faɗa sai dai a Hai'ala biyu kawai, sai ya ce: "Babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah".