عَنْ عَبْدِ اللهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنها أَنَّهُ سَمِعَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ:
«إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ، ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَنْبَغِي إِلَّا لِعَبْدٍ مِنْ عِبَادِ اللهِ، وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ أَنَا هُوَ، فَمَنْ سَأَلَ لِيَ الْوَسِيلَةَ حَلَّتْ لَهُ الشَّفَاعَةُ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 384]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 384]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nuna wa wanda ya ji mai kiran sallah da ya maimaita a bayansa, sai ya faɗi irin abinda ya fada, ban da Hai'ala biyu, cewa ya ce a bayansu: Babu dabara ba ƙarfi sai ga Allah.
Sannan ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan gama kiran sallah, domin cewa wanda ya yi salati ɗaya a gare shi to Allah zai yi masa salati goma da shi, ma'anar salatin Allah ga bawanSa: shi ne YabonSa ga bawa a wurin Mala'iku.
Sannan ya yi umarni da a roƙa masa Allah Wasila - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ita ɗin wani matsayi ne a aljanna, shi ne mafi ƙololuwa, ba ta dace ba, kuma wannan matsayin ba zai samu ba sai ga wani bawa ɗaya daga dukkanin bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, ina ƙaunar in zama ni ne shi, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗa ne, don Tawalu’u; domin cewa idan shi wannan matsayin da yake babba ba zai kasance ba sai ga mutum ɗaya, to, ai wannan mutum ɗayan ba zai zama ba sai shi (Annabin) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin shi ne mafificin halitta.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa wanda ya roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila; to, cetonsa zai same shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.