عن أنس بن مالك رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«مَنْ نَسِيَ صَلَاةً فَلْيُصَلِّ إِذَا ذَكَرَهَا، لَا كَفَّارَةَ لَهَا إِلَّا ذَلِكَ: {وَأَقِمِ الصَّلاةَ لِذِكْرِي} [طه: 14]».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 597]
المزيــد ...
Daga Anas Ɗan Malik Allah Ya yarda da shi, daga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Wanda ya manta wata sallah, to, ya sallaceta idan ya tunata, babu kaffara gareta sai hakan: {Ku tsai da sallah domin tunani} [Daha: 14".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 597]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayya cewa wanda ya mance yin kowacce sallar farilla har lokacinta ya fita, to, ya wajaba a kansa ya yi gaggawar ramata a duk lokacin da ya tunata, babu gogewa ko suturtawa ga laifin barinta sai dai kawai musulmi ya sallaceta a yayin da ya tunata, Allah Ya faɗa a littafinSa Mai girma: {Ka tsai da sallah domin tunaNi} [Daha: 14], wato: Ka tsai da sallar daka manta idan ka tunata.