عن عَائِشَةَ رضيَ الله عنها قالت: إِنِّي سمعْتُ رسولَ الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«لَا صَلَاةَ بِحَضْرَةِ الطَّعَامِ، وَلَا هُوَ يُدَافِعُهُ الْأَخْبَثَانِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 560]
المزيــد ...
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 560]
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana sallah in a wurin akwai abincin da ran mai sallah yake sha'awarsa, kuma zuciyarsa take rataye da shi.
Haka nan ya hana sallah tare da matse najasa biyu - su ne fitsari da bahaya -, saboda shagaltuwa da matse najasar.