عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ:
أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ السَّاعَةِ، فَقَالَ: مَتَى السَّاعَةُ؟ قَالَ: «وَمَاذَا أَعْدَدْتَ لَهَا». قَالَ: لاَ شَيْءَ، إِلَّا أَنِّي أُحِبُّ اللَّهَ وَرَسُولَهُ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: «أَنْتَ مَعَ مَنْ أَحْبَبْتَ». قَالَ أَنَسٌ: فَمَا فَرِحْنَا بِشَيْءٍ، فَرِحْنَا بِقَوْلِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أَنْتَ مَعَ مَنْ أَحْبَبْتَ» قَالَ أَنَسٌ: فَأَنَا أُحِبُّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَبَا بَكْرٍ، وَعُمَرَ، وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ مَعَهُمْ بِحُبِّي إِيَّاهُمْ، وَإِنْ لَمْ أَعْمَلْ بِمِثْلِ أَعْمَالِهِمْ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 3688]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 3688]
Wani mutumin karkara irin waɗanda suke zama a sahara ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: game da lokacin tashin alkiyama?
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Meka tanadar mata na aiki na gari?
Sai mai tambayar ya ce: Ban tanadi wani aiki mai yawa ba sai dai ni ina son Allah da ManzonSa, bai ambaci wanin hakan ba daga ayyuaka na zuciya da jiki da dukiya; domin su dukkaninsu rassa ne ga soyayya masu jerantuwa ne akanta, kuma domin soyayya ta gaskiya tana zaburar da kokarin yin aiki na gari.
Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi Ya ce masa: Lallai kai kana tare da wanda ka so a aljanna.
Sai sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka yi farin ciki mai girma da wannan busharar.
Sannan Anas ya bada labarin cewa shi yana son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma yana kaunar ya kasance tare da su, koda aikinsa bai zama irin aikinsu ba.