عن أبي بَكرة رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«إِذَا الْتَقَى الْمُسْلِمَانِ بِسَيْفَيْهِمَا فَالْقَاتِلُ وَالْمَقْتُولُ فِي النَّارِ»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ هَذَا الْقَاتِلُ، فَمَا بَالُ الْمَقْتُولِ؟ قَالَ: «إِنَّهُ كَانَ حَرِيصًا عَلَى قَتْلِ صَاحِبِهِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 31]
المزيــد ...
Daga Abu Bakrata - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, to, wanda ya kashe da wanda aka kashe suna cikin wuta", sai na ce: Ya Manzon Allah, wannan mai kisan ne, to, mene ne laifin wanda aka kashe? ya ce: "Lallai shi ma ya kasance mai kwaɗayi ne a kan kashe ɗan uwansa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 31]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba da labarin cewa idan musulmai biyu suka haɗu da takubbansu, kowanne daga cikinsu yana nufin kashe abokinsa, to, mai kisan yana cikin wuta saboda kashe abokinsa, sahabbai suka rikita ga wanda aka kashe; Ta yaya zai zama a wuta? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa shi ma yana wuta don kwaɗayinsa a kan kashe ɗan uwansa, babu abin da ya hanashi kisan sai gaggawar mai kisan da kuma rigayarsa da yayi.