+ -

عَنْ مُعَاذِ بْنِ جَبَلٍ رضي الله عنه قَالَ:
كُنْتُ مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَأَصْبَحْتُ يَوْمًا قَرِيبًا مِنْهُ وَنَحْنُ نَسِيرُ، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ أَخْبِرْنِي بِعَمَلٍ يُدْخِلُنِي الجَنَّةَ وَيُبَاعِدُنِي عَنِ النَّارِ، قَالَ: «لَقَدْ سَأَلْتَنِي عَنْ عَظِيمٍ، وَإِنَّهُ لَيَسِيرٌ عَلَى مَنْ يَسَّرَهُ اللَّهُ عَلَيْهِ، تَعْبُدُ اللَّهَ وَلاَ تُشْرِكْ بِهِ شَيْئًا، وَتُقِيمُ الصَّلاَةَ، وَتُؤْتِي الزَّكَاةَ، وَتَصُومُ رَمَضَانَ، وَتَحُجُّ البَيْتَ» ثُمَّ قَالَ: «أَلاَ أَدُلُّكَ عَلَى أَبْوَابِ الخَيْرِ: الصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَالصَّدَقَةُ تُطْفِئُ الخَطِيئَةَ كَمَا يُطْفِئُ الْمَاءُ النَّارَ، وَصَلاَةُ الرَّجُلِ مِنْ جَوْفِ اللَّيْلِ» قَالَ: ثُمَّ تَلاَ: «{تَتَجَافَى جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ}، حَتَّى بَلَغَ {يَعْمَلُونَ}» ثُمَّ قَالَ: «أَلاَ أُخْبِرُكَ بِرَأْسِ الأَمْرِ كُلِّهِ وَعَمُودِهِ، وَذِرْوَةِ سَنَامِهِ؟» قُلْتُ: بَلَى يَا رَسُولَ اللهِ، قَالَ: «رَأْسُ الأَمْرِ الإِسْلاَمُ، وَعَمُودُهُ الصَّلاَةُ، وَذِرْوَةُ سَنَامِهِ الجِهَادُ» ثُمَّ قَالَ: «أَلاَ أُخْبِرُكَ بِمَلاَكِ ذَلِكَ كُلِّهِ؟» قُلْتُ: بَلَى يَا نَبِيَّ اللهِ، فَأَخَذَ بِلِسَانِهِ قَالَ: «كُفَّ عَلَيْكَ هَذَا» فَقُلْتُ: يَا نَبِيَّ اللهِ، وَإِنَّا لَمُؤَاخَذُونَ بِمَا نَتَكَلَّمُ بِهِ؟ فَقَالَ: «ثَكِلَتْكَ أُمُّكَ يَا مُعَاذُ، وَهَلْ يَكُبُّ النَّاسَ فِي النَّارِ عَلَى وُجُوهِهِمْ أَوْ عَلَى مَنَاخِرِهِمْ إِلاَّ حَصَائِدُ أَلْسِنَتِهِمْ».

[صحيح بمجموع طرقه] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 2616]
المزيــد ...

Daga Mu'az Bin Jabal -Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har yakai {Suke aikatawa}". Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".

- - [سنن الترمذي - 2616]

Bayani

Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna kan tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar da ni aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, Ya ce: Haƙiƙa ka tambayeni daga wani aiki mai girman aikatawa ga rayuka, kuma mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa; ka yi farillan Musulunci:
Na farko: Ka bauta wa Allah Shi kaɗai kada ka taranya wani abu da Shi.
Na biyu: Ka tsaida salloli biyar na farilla a yini da dare: Asuba, da Azahar, da La'asar, da Magariba, da Isshai, da sharuɗɗansu da rukunansu da wajibansu.
Na uku: Ka fitar da zakkar farilla, ita ce ibada ta dukiya wajiba a kowace dukiyar da takai wani gwargwado abin iyakancewa a shari'a, ana bada ita ga waɗanda suka cancanceta.
Na huɗu: Ka azimci Ramadan, shi ne kamewa daga ci da sha da wasunsu daga abubuwan da suke karya azimi da niyyar bauta, daga ɓollowar alfijir zuwa faɗuwar rana.
Na biyar: Ka ziyarci Ɗakin Allah, da nufin Makka dan yin ibadun aikin Hajji, dan bauta ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na sanar da kai hanya mai kaiwa ga ƙofofn alheri ba? hakan da bin waɗancan farillan da nafilfilin:
Na farko: Azimin nafila, shi mai hanawa ne daga afkawa cikin saɓo, hakan da karya sha'awa, da kuma rage ƙarfi.
Na biyu: Sadakar nafila tana kashe laifuka bayan an aikata su kuma tana tafiyar da su tana kuma shafe su.
Na uku: Sallar dare a ɗaya bisa uku na ƙarshe, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta faɗinSa - Maɗaukakin sarki -: {Sasanninsu suna nisanta} wato: Suna nisanta {Daga makwantansu} wato: Wuraren kwana { Suna kiran Ubangijinsu} da yin sallah da zikiri da karatu da addu'a, {Dan tsoro da kwaɗayi kuma suna ciyarwa daga abinda muka azirta su, wata rai bata sanin abinda aka ɓoye musu na abinda ido yake farin ciki da shi} wato abinda idanunsu zasu yi farin ciki da shi a ranar Alƙiyama da kuma aljanna ta ni'ima, {Dan sakamako da abinda suka kasance suna aikatawa}.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin bana baka labari da asalin Addini ba? da ginshiƙinsa wanda yake dogaro akansa? da ƙololuwar tozansa?
Mu'az - Allah Ya yarda ad shi - ya ce: Eh, ya Manzon Allah.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Asalin al'amari: Musulunci shi ne shaidawa biyu, kuma dasu ne tushen Addini zai wayi gari tare da mutum. Ginshiƙinsa: Sallah, babu Musulunci ba tare da sallah ba, kamar yadda babu gida ba tare da ginshiƙi ba, wanda ya yi sallah Addininsa zai ƙarfafa zai ɗaga; kuma ƙololuwar tozansa da ɗaukakarsa yana kasancewa ne da yin yaƙi da yin ƙoƙari a yaƙar maƙiya Addini dan ɗaukaka kalmar Allah.
Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin ba na baka labari da kyautata abinda ya gabata ba? sai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe harshensa, ya ce: Ka hana wannan kada ka yi magana da abinda bai shafeka ba. Mu'az ya ce: Shin Ubangijinmu zai kamamu Ya yi mana hisabi da dukkan abinda muke magana da shi?!
Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Mahaifiyarka ta yi wabinka! ba ana nufin mummunar addu'a akansa ba, sai dai yana daga zancen larabawa dan faɗakar da shi zuwa wani al'amarin da ya kasance yana kamata ya farka da shi ya kuma san shi, sannan ya ce: Ai babu abinda yake afka mutane ya jefasu cikin wuta ta fuskokinsu sai abinda harasansu suke girba na kafirci da ƙazafi da zagi da yi da mutum da annamimanci da ƙagen ƙarya da makamancinsu.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية الرومانية Malagasy Oromo
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kwaɗayin sahabbai - Allah Ya yarda da su - akan ilimi, saboda haka ne tambayar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - take yawaita daga garesu.
  2. Fiƙihun sahabbai - Allah Ya yarda da su - dan saninsu cewa ayyuka sababi ne na shiga aljanna.
  3. Tambayar data fito daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - tambaya ce mai girma; domin cewa shi a haƙiƙa shine sirrin rayuwa da samuwa, dukkan samamme a cikin wannan rayuwar ta duniya daga 'ya'yan Adam ko daga aljanu ƙarshensa kodai aljanna ko wuta, saboda haka ne wannan tambayar ta zama mai girma.
  4. Jeranta shigarsa aljanna akan zuwa da rukunan Musulunci guda biyar, su ne: Shaidawa biyu da Sallah da Zakka da Azimi da Hajji.
  5. Asalin Addini kuma mafi tsadar abubuwa muhimmai kuma mafi ɗaukakar wajibai (su ne) kaɗaita Allah, da bauta maSa Shi kaɗai baShi da abokin tarayya.
  6. Rahamar Allah ga bayinSa cewa Ya buɗe musu ƙofofin alheri dan su yi guziri daga sabubban lada da gafarta zunubai.
  7. Falalar neman kusanci da nafilfili bayan yin farillai.
  8. Sallah a cikin Musulunci kamar ginshiƙin da runfa take tsaye a kansa ne, Musulunci yana tafiya ne da tafiyata, kamar yadda runfa take faɗuwa da faɗuwar ginshiƙinta.
  9. Wajabcin kiyaye harshe daga abinda zai cutar da mutum a cikin Addininsa.
  10. Kame harshe da kiyaye shi da tsare shi shi ne asalin alheri gaba ɗayansa.