عن ابن عباس -رضي الله عنهما-: أن رسول الله -صلى الله عليه وسلم- لما بعث معاذا إلى اليمن قال له: "إنك تأتي قوما من أهل الكتاب، فليكن أولَ ما تدعوهم إليه شهادة أن لا إله إلا الله" -وفي رواية: "إلى أن يوحدوا الله-، فإن هم أطاعوك لذلك فأعلمهم أن الله افترض عليهم خمس صلوات في كل يوم وليلة، فإن هم أطاعوك لذلك فأعلمهم أن الله افترض عليهم صدقة تؤخذ من أغنيائهم فَتُرَدُّ على فقرائهم، فإن هم أطاعوك لذلك فإياك وكَرَائِمَ أموالِهم، واتق دعوة المظلوم فإنه ليس بينها وبين الله حجاب".
[صحيح.] - [متفق عليه.]
المزيــد ...

Daga Dan Abbas cewa Annabi yayin da Annabi ya tura Mu'az Yamen ya ce masa: "Lallai cewa kai zaka je wajen wasu Mutane na Ma'abota littafi, to farkon abinda zaka fara kiransu akai shi ne Shaidawa Babu Wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa da gaskiya sai Allah" a cikin wata Riwayar kuma: "Kan su kadaita Allah" Idan suka bika to ka sanar da su cewa Allah ya wajabta musu Salloli biyar a wuni da dare, Idan suka bika ka sanar da su cewa Allah ya Wajbata musu Zakka Wacce za'a rika karba daga mawadatansu a bawa Talakawansu, to idan suka bika kan hakan, to babu kai babu Dukiyoyinsu masu Daraja, kuma ka guji Adduar wanda aka zalunta cewa batada wani Hijabi Tsakninta da Allah"
Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi

Bayani

Cewa Annabi yayin da ya nusar da Mu'az Dan Jabal zuwa yankin Yeman yana mai kira zuwa ga Allah kuma mai koyarwa kuma ya zana masa tsarin da zai saukake masa wajen kiransa, kuma yayi masa bayani cewa zai gamu da wasu Mutane Ma'abota Ilimi kuma Masu Jidali daga cikin Yahudawa da kuma Kiristoci, don ya zamanto yana shirye da jayayya da su da kuma kautar da shubharsu, kuma sannan ya fara kiransa da abinda yafi Muhimmanci sannan wanda yake binsa kuma ya kirawo Mutane zuwa su gyara Akidarsu da fari wanda hakan shi ne Tushe, idan sukai biyayya kan hakan sai ya Umarce su da tsaida Sallah domin ita ce Mafi girman Wajibi bayan tauhidi, idan suka yarda da hakan sai ya Umarci Mawadatansu da bayar da Zakkar Dukiyoyinsu ga Talakawansu don dauke musu radadin abinda yake damunsu da kuma godiya ga Allah sannan ya ja kunnensa ga barin mafi tsadar Dukiyarsu domin Wajibi a ciki shi ne mtsakaiciya, sannan ya kwadaitar da shi akan Adalci da kuma barin zalunci don kada Addu'ar wanda aka Zalunta don amsashiya ce.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Uighur Kurdawa
Manufofin Fassarorin