عن عبد الله بن الشخير رضي الله عنه قال: "انطلقت في وفد بني عامر إلى رسول الله صلى الله عليه وسلم فقلنا: أنت سيدنا. فقال السيد الله -تبارك وتعالى-. قلنا: وأَفْضَلُنَا فَضْلًا وأَعْظَمُنْا طَوْلًا. فقال: قولوا بقولكم أو بعض قولكم، ولا يَسْتَجْرِيَنَّكُمُ الشيطان".
[صحيح] - [رواه أبو داود وأحمد]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Ashukir -Allah ya yarda shi- "Na tafi a cikin wata tawaga ta Banu Amir zuwa ga Annabi sai muka ce da shi: Kaine shugaban mu sai ya ce: Allah shi ne Shugaba, sai muka ce: Kuma kaine mafi falalarmu kuma kaine mafi Matsayi, sai ya ce: Ku fadi Maganarku amma kada Shaidan dai ya samu dama ta hanyarku.
Ingantacce ne - Abu Daud Ya Rawaito shi

Bayani

Yayin da wannan Tawaga suka kai Matuka wajen Yabon Annabi sai ya hana su haka; don ladabi ga Allah da kuma kare Tauhidinsu, kuma ya umarce su kan su takaita akan lafazan da babu shige gona da iri a cikinsu kuma babu laifi cikinsu;kamar su kirawo shi Da Muhammadu Manzon Allah kamar yadda Allah ya kirashi da shi, kuma ya ja kunnensu kan kada su zamanto wakilan Shaidan cikin ayyukan da zasu sa musu waswasi akansa.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Swahili bushtu Asami السويدية الأمهرية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin