عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ رضي الله عنهما أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«أُعْطِيتُ خَمْسًا لَمْ يُعْطَهُنَّ أَحَدٌ قَبْلِي: نُصِرْتُ بِالرُّعْبِ مَسِيرَةَ شَهْرٍ، وَجُعِلَتْ لِي الأَرْضُ مَسْجِدًا وَطَهُورًا، فَأَيُّمَا رَجُلٍ مِنْ أُمَّتِي أَدْرَكَتْهُ الصَّلاَةُ فَلْيُصَلِّ، وَأُحِلَّتْ لِي المَغَانِمُ، وَلَمْ تَحِلَّ لِأَحَدٍ قَبْلِي، وَأُعْطِيتُ الشَّفَاعَةَ، وَكَانَ النَّبِيُّ يُبْعَثُ إِلَى قَوْمِهِ خَاصَّةً وَبُعِثْتُ إِلَى النَّاسِ عَامَّةً».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 335]
المزيــد ...
Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba : An bani cin nasara ta hanyar tsoro (da ake jefawa abokan gaba) wata daya (gabanin haduwar mu), kuma an sanya mini kasa ta zama wajen yin sallah ta kuma mai tsarkakewa, don haka duk wanda sallah ta riske shi cikin al'umma ta to sai ya yi ta, kuma an halarta min ganima, ba'a taba halartawa wani kafin ni ba, kuma an bani ceto, ya kasance ana aiko Annabi zuwa ga mutanensa kadai , ni kuwa an aiko ni zuwa ga mutane baki daya".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 335]
Annbai - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Ya ba shi wasu dabi'u uku (wadanda) bai bada su ga wani daga Annabwa a gabnina ba.
Na farko: An bani nasara da tsoro da za'a jefa shi a cikin zukatan maƙiyana koda tsakanina da su akwai tafiyar wata.
Na biyu: An sanya mana ƙasa ta zama masallacin da zamu dinga sallah a duk inda muke, kuma mai tsarkakewa da turɓaya a yayin rasa ruwa, ko gaza anfani da shi.
Na uku: An halatta mana ganimomin yaƙi, sune waɗanda musulmai suke ɗiba a yaƙoƙinsu tare da kafirai.
Na huɗu: An bani ceto mafi girma dan hutar da mutane daga firgicin tsayuwa a ranar Alkiyama.
Na biyar: An aikoni zuwa halitta gaba ɗaya mutanensu da Aljanunsun, saɓanin Annabawa kafin ni sun kasance ana aikosu ne zuwa mutanensu ne kawai.