عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه عَنْ رَسُولِ اللهِ صلى الله عليه وسلم أنه قال:
«وَالَّذِي نَفْسُ مُحَمَّدٍ بِيَدِهِ لَا يَسْمَعُ بِي أَحَدٌ مِنْ هَذِهِ الْأُمَّةِ يَهُودِيٌّ وَلَا نَصْرَانِيٌّ، ثُمَّ يَمُوتُ وَلَمْ يُؤْمِنْ بِالَّذِي أُرْسِلْتُ بِهِ إِلَّا كَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّارِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 153]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Na rantse da wanda ran Muhammad yake a hannunSa , babu wani daya daga wannan al'ummar da zai ji ni Bayahude ne ko Kirista, sannan ya mutu bai yi imani da abinda aka aikoni da shi ba sai ya zama cikin 'yan wuta".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 153]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana rantsuwa da Allah cewa wani daya daga wannan al'ummar ba zai ji shi ba, Bayahude ne ko Kirista ko waninsu (ba zai ji) kiran Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya isa zuwa gare shi ba, sannan ya mutu bai yi imani da shi ba sai ya zama daga 'yan wuta yana madawwami a cikinta har abada.