عَنِ ابْنِ مَسْعُودٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ:
قَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنُؤَاخَذُ بِمَا عَمِلْنَا فِي الْجَاهِلِيَّةِ؟ قَالَ: «مَنْ أَحْسَنَ فِي الْإِسْلَامِ لَمْ يُؤَاخَذْ بِمَا عَمِلَ فِي الْجَاهِلِيَّةِ، وَمَنْ أَسَاءَ فِي الْإِسْلَامِ أُخِذَ بِالْأَوَّلِ وَالْآخِرِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6921]
المزيــد ...
Daga Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi- ya ce:
Wani mutum ya ce: ya Manzon Allah, shin za'a kamamu da abinda muka aikata a lokacin Jahiliyya? ya ce: "Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6921]
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana falalar shiga Musulunci. Kuma cewa wanda ya musulunta kuma ya kyautata Musuluncinsa ya zama mai tsarkakewa mai gaskiya, to ba za’a yi masa hisabi da abinda ya aikata na sabo ba a lokacin Jahiliyya, Wanda ya munana a cikin Musulunci, da ya zama munafiki ko ya yi ridda ga Addininsa, za'a yi masa hisabi da abinda ya aikata a cikin kafirci, da kuma abinda ya aikata a cikin Musulunci.