عن أبي سعيد الخُدْريِّ رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«‌مَنْ ‌رَأَى ‌مِنْكُمْ ‌مُنْكَرًا فَلْيُغَيِّرْهُ بِيَدِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِلِسَانِهِ، فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ فَبِقَلْبِهِ، وَذَلِكَ أَضْعَفُ الْإِيمَانِ».

[صحيح] - [رواه مسلم]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'id Al-Kudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana cewa:
"Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani".

Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin umarni da canza abin ki - shi ne dukkanin abinda Allah da ManzonSa suka hana - gwargwadon iko, Idan ya ga wani abin ki to yana wajaba akansa ya canja shi da hannu idan yana da iko, Idan ya gajiya ga hakan, to ya canja shi da harshensa, ta hanyar hana mai aikatawar, kuma ya bayyana masa cutar hakan, ya kuma shiryar da shi zuwa alheri maimakon wannan sharrin, Idan ya gajiya daga wannan matakin, to ya canja shi da zuciyarsa shi ne ya ki wannan mummunan aikin, kuma ya yi niyyar cewa shi da yana da iko akan canja shi to da ya aikata, canjawa da zuciya shi ne mafi raunin matakan imani a canja abin ki.

Fassara: Turanci Fassara Yaren Faransanci Sifaniyanci Turkiyanci urdu Indonisiyanci Bosniyanci Rashanci Fassarar Bangaliyanci Fassara da Yaren Chanise Farisanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Sinhalese Uighur Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية الدرية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Hadisn asali ne a bayanin matakan canja abin ki.
  2. Umarni da bi sannu-sannu a hani ga abin ki, kowa gwargwadon iyawarsa da ikonsa.
  3. Hani daga abin ki wani babi ne mai girma a Addini kuma ba ya saraya akan wani mutum, kuma ana dorawa kowanne musulmi shi gwargwadon ikonsa.
  4. Umarni da aikin alheri da hani daga abin ki yana daga dabi'un imani, kuma imani yana karuwa yana kuma raguwa.
  5. Ana sharadantawa a hani daga abin ki: Sanin cewa wannan aikin abin ki ne.
  6. Ana sharadantawa a canja abin ki: Cewa kada wani abin kin mafi girma daga gare shi ya biyo baya.
  7. Akwai wasu ladubba da sharuddan da yake kamata ga musulmi ya sansu ga hani daga abin ki.
  8. Hani daga abin ki yana bukatuwa zuwa ga siyasa ta shari'a, kuma da ilimi da basira.
  9. Rashin inkari da zuciya yana nuni ga raunin imani.