kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

Imani tsagi saba’in- ko Sittin- da wani abu ne, mafi falalarsu faɗin: Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, mafi ƙasa kuma kawar da ƙazanta daga hanya
عربي Turanci urdu
Wanda ya ga wani mummunan abu daga cikinku, to ya canza shi da hannunsa, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da harshe, idan ba zai iya ba to (ya canza shi) da zuciyarsa, wannan shi ne mafi raunin imani
عربي Turanci urdu
Wanda ya kyautata a Musulunci ba za'a kama shi da abinda ya aikata ba a lokacin Jahiliyya, wanda kuma ya munana a cikin Musulunci za'a kama shi da na farko da na karshe
عربي Turanci urdu
Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi
عربي Turanci urdu
Musulmi shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa da hannunsa, wanda ya yi hijira shi ne wanda ya kauracewa abinda Allah Ya yi hani daga gare shi
عربي Turanci urdu
Mu muna ji a cikin zuciyarmu abinda da dayan mu zai fada to da yana da girma, ya ce: "Kuma hakika kun same shi ?" Suka ce: Eh, ya ce: "Wannan shi ne imani baro-baro
عربي Turanci urdu
Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku
عربي Turanci urdu
Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo
عربي Turanci Indonisiyanci