عَنِ الْعَبَّاسِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ رضي الله عنه أَنَّهُ سَمِعَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، يَقُولُ:
«ذَاقَ طَعْمَ الْإِيمَانِ مَنْ رَضِيَ بِاللهِ رَبًّا، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولًا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 34]
المزيــد ...
Daga Abbas ɗan Abdulmuɗɗalib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Ya ɗanɗani ɗanɗanon imani wanda ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da Musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammadu a matsayin Manzo".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 34]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa mumini mai gaskiya a cikin imaninsa wanda zuciyarsa ta nutsu da shi zai samu kuma zai riska a cikin zuciyarsa buɗi da yalwa da farin ciki da zaƙi, da jin daɗin kusanci ga Allah - Maɗaukakin sarki - idan ya yarda da abu uku:
Na farko: Ya yarda da Allah a matsayin Ubangiji, hakan ƙirjinsa ya buɗe ga abinda zai zo masa daga Allah da hukuncin Rububiyyah na raba arzuƙa da halaye, ba zai samu bijirewa ba a cikin zuciyarsa akan wani abu daga hakan, kuma bai nemi wani Ubangiji wanin Allah - Maɗaukakin sarki ba.
Na biyu: Ya yarda da musulunci a matsayin addini, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe ga abinda musulunci ya ƙunsa na takalif da wajibai, bai tafi zuwa wanin hanyar Musulunci ba.
Na uku: Ya yarda da (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a matsayin Manzo, hakan shi ne ƙirjinsa ya buɗe kuma ya yi farin ciki da dukkan abinda ya zo da shi ba tare da wani kaikawo ko kokwanto ba, bai shiga (wata hanya ba) sai abinda ya dace da shiriyar Manzonsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.