عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المُؤْمِنينَ رَضِيَ اللهُ عَنْها قَالَتْ:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا أَمَرَهُمْ أَمَرَهُمْ مِنَ الأَعْمَالِ بِمَا يُطِيقُونَ، قَالُوا: إِنَّا لَسْنَا كَهَيْئَتِكَ يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّ اللَّهَ قَدْ غَفَرَ لَكَ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ، فَيَغْضَبُ حَتَّى يُعْرَفَ الغَضَبُ فِي وَجْهِهِ، ثُمَّ يَقُولُ: «إِنَّ أَتْقَاكُمْ وَأَعْلَمَكُمْ بِاللَّهِ أَنَا».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 20]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarce su da wasu ayyukan yana umartar su da abin da zasu iya, suka ce: Lallai mu bamu kasance kamar yanayinka ba ya Manzon Allah, lallai Allah Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: «Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa».
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 20]
Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - tana bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai umarci mutane da wani aiki cikin ayyuka sai ya umarce su da abin da zai yi musu sauƙi banda wanda zai wahalar da su, dan jin tsoron kada su gajiya daga dawwama a kansa, sai ya yi aikin da shine kishiyar abin da yake umartarsu da shi daga sauƙaƙawa, sai dai cewa su sun nemi taklifin abin da zai wahalar da su daga gare shi, dan sun ƙudirce buƙatuwarsu zuwa kai matuƙa a cikin aikin dan ɗaukaka darajoji koma bayansa. Sai su ce: Lallai halinmu ba kamar halinka ba ne ya Manzon Allah, domin Allah haƙiƙa Ya gafarta maka abin da ya gabata daga zunubinka da abin da ya jinkirta, sai ya yi fushi har sai da aka gane fushi a fuskarsa, sannan ya ce: Lallai ni na fiku tsoron Allah kuma na fiku saninSa, dan haka ku aikata abin da nake umartarku da shi.