عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ رضي الله عنهما قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ الْإِيمَانَ لَيَخْلَقُ فِي جَوْفِ أَحَدِكُمْ كَمَا يَخْلَقُ الثَّوْبُ الْخَلِقُ، فَاسْأَلُوا اللَّهَ أَنْ يُجَدِّدَ الْإِيمَانَ فِي قُلُوبِكُمْ».
[صحيح] - [رواه الحاكم والطبراني] - [المستدرك على الصحيحين: 5]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Lallai imani yana tsufa a zukatan dayanku kamar yadda tsohon tufafi yake tsufa, ku roki Allah Ya sabunta imani a cikin zukatanku".
[Ingantacce ne] - - [المستدرك على الصحيحين - 5]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa imani yana tsufa a cikin zuciyar musulmi kuma yana rauni kamar sabon tufafin da yake tsufa saboda tsawon amfani da shi. Saboda yankewa a ibada, ko aikata sabo da afkawa a cikin sha'awowi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da cewa mu roki Allah - Madaukakin sarki - ya sabunta imaninmu, ta hanayar tsayuwa da wajibai da yawan zikiri da istigfari.