عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«مَثَلُ الْمُنَافِقِ، كَمَثَلِ الشَّاةِ الْعَائِرَةِ بَيْنَ الْغَنَمَيْنِ تَعِيرُ إِلَى هَذِهِ مَرَّةً وَإِلَى هَذِهِ مَرَّةً».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2784]
المزيــد ...
Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2784]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin munafiki kuma shi kamar akuya ce mai kaikawo, ba ta san wanne garke za ta bi ba na tumakai, Tana tafiya zuwa wannan garken wani lokaci, da kuma zuwa wani garken a wani lokacin daban, Su masu dimuwane tasakanin imani da kafirci, su ba sa tare da muminai a zahiri da badini, kuma su ba sa tare da kafirai a zahiri da badini, su dai zahirinsu suna tare da muminai, kuma badininsu suna cikin kokwanto da taraddudi, wani lokaci yana karkata zuwa ga wadannan, wani lokacin kuma zuwa ga wadannan.