+ -

عَنْ سُفْيان بنِ عَبْدِ اللهِ الثَّقَفِيّ رضي الله عنه قال:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، قُلْ لِي فِي الْإِسْلَامِ قَوْلًا لَا أَسْأَلُ عَنْهُ أَحَدًا غَيْرَكَ، قَالَ: «قُلْ: آمَنْتُ بِاللهِ، ثُمَّ اسْتَقِمْ».

[صحيح] - [رواه مسلم وأحمد] - [مسند أحمد: 15416]
المزيــد ...

Daga Sufyan Dan Abdullah AlSakafi - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".

[Ingantacce ne] - - [مسند أحمد - 15416]

Bayani

Sahabi Sufayanu dan Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da ya sanar da shi wata magana mai tattaro ma'anonin Musulunci, da zai yi riko da ita, wacce ba zai tambayi waninsa game da ita ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka ce: Na kadaita Allah, kuma na yi imani da cewa Shi ne Ubangijina kuma Allah na, Mahaliccina, Abin bautata na gaskiya ba Shi da abokin tarayya, Sannan ya jawu ga biyayya ga Allah ta hanyar bada farillan Allah, da barin abubuwan da Allah Ya haramta, ya kuma ci gaba akansu.

Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Vietnam Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية التشيكية الموري Malagasy Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Asalin Addini shi ne imani da Allah da UbangidantakarSa da AllantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
  2. Muhimmancin tabbatuwa bayan imani, da kuma ci gaba a cikin ibada, da tabbata akan hakan.
  3. Imani sharadi ne na karbar ayyuka.
  4. Imani da Allah, ya kunshi abinda kudire shi yake wajaba daga akidun imani da tushensu, da abinda yake bin hakan, daga ayyukan zuciyoyi, da jawuwa da mika wuya ga Allah a badini da zahiri.
  5. Tabbatuwa lazimtar hanya ce, ta hanyar aikata wajibai da barin abubuwan da aka hana.
Kari